Connect with us

NAZARI

Shekara daya A Mulki: Gwamna Matawalle Ya Ciri Tuta, Inji Tukur danfulani Gusau

Published

on

A hakikanin gaskiya, bikin murnar cika shekara daya a karagar mulki ba abu ba ne karami ga dukkanin wata gwamnati da ke kan mulki ba, musamman saboda za’a waiwaya baya domin duba ga abubuwan ci gaba da gwamnatin ta cimma. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Shugaban Jam’iyyar PDP reshen karamar hukumar Gusau, ALHAJI TUKUR dANFULANI GUSAU, a yayin da yake zantawa da manema labarai dangane da cikar Gwamnan Jihar Zamfara Alhaj Dakta Bello Matawalle Maradun Shekara daya a bisa kujerar mulki.
Alhaji Tukur danfulani Gusau ya ci gaba da bayyana cewa, “Idan akayi duba da Gwamnatin Dakta Bello Mohammed Matawallen Maradun, kan cikar Gwamna shekara daya a karagar mulki, musamman idan aka yi la’akari da yadda Al’ummar Jihar Zamfara ke nuna matukar godiyarsu ga mai Girma Gwamna, a bisa Namijin kokarin da gwamnan ya yi na canja fuskar Jihar Zamfara, daga mummunar fuska zuwa kyakkyawa fuska a cikin shekara daya kacal. Tabbas Mutanen Zamfara na matukar farin cikinsu da wannan samun nasara da gwamnan ya kawo.”
Shugaban Jam’iyyar PDP na karamar hukumar Gusau ya ci gaba da cewa, “Gwamnatin Matawalle ta samu nasarori wadanda ba zasu iya lissafuwa ba, wanda kuma idan Mutane za suyi duba da su, jajartacciyar gwamanati ce kadai za ta iya samar da wadannan abubuwa.”

Ya kara da bayyana cewa, “Idan aka dauki bangaren tsaro, tabbas Gwamna Matawalle ya samu gagarumin nasara maras misaltuwa, musamman idan aka duba kamin zuwan gwamnan yadda matsala tsaro ya tabarbare a lokacin Gwamnatin baya, wanda a halin yanzu Mutanen Jihar na mashi kallon wanda suka dade suna addu’ar su sami irinsa domin ya yi masu mulkin jihar.”
Alhaji Tukur danfulani Gusau ya kara da bayyana cewa, “Haka zalika, Gwamnatin Gwamna Bello Matawalle, ta yi hubbasa wurin samu nasara a bangaren ilimi, samar da sana’oi domin kawar da talauci, samar da ddimbin ayyukan yi ga Matasan Jihar dimbin Mata da Maza, sannan da inganta albashin Ma’aikata Jihar baki daya, inganta bangaren kiwon lafiya, musamman samar da Ma’aikatar gaggawa domin dakile mummunar cutar Annobar korona a Jihar ta Zamfara.”
danfulani Gusau ya kara da bayyana cewa, “Sannan Gwamna Bello Matawalle Mutum ne mai son zaman lafiya da kwamishinoninsa da sauran mukarraban Gwamnatinsa baki daya, shiyasa za’a ya basu damar da ya kamata domin su ci gaba da yin aiki tukuru domin ganin sun kawo samarwa Jihar abubuwan morewa rayuwa da ci gaban Jihar baki daya.”
Shugaban Jam’iyyar PDP na Gusau, ya ce, “Abin da Mutane ba su sani ba game da Gwamna Matawalle Maradun, shi ne, a cikin gwamnatinsa ba wadanda suke Jam’iyya daya kawai yake mu’amala da su kadai ba, har wadanda ke Jam’iyyar ta Adawa ma, gwamnan ya janyo su a jiki ana tafiya tare, musamman wadanda ke cikin Jam’iyyar ta adawa wato APC, wadanda ko a lokacin baya su sam basu yarda su goyi bayan tafiyar Tsohon Gwamnan da ya sauka ba, wato Abdulazeez Yari. A bisa wannan dalili ne na ganin cewa ra’ayinsu na son ci gaban Jihar yazo daya da irin nashi manufofin, shiyasa ya janyo su a jiki domin tafiyar tasu ta zama iri daya, ma’ana shi ne, a hannu waje daya domin kawo ma Jihar Zamfara ci gaba baki daya.”
danfulani Gusau ya kara da fashin bakin cewa, “Wadannan ‘Yan Jam’iyyar APC da ke tare da Gwamna Matawalle, su ne wadanda suka tabbatar da cewa sun kai Gwamnatin Abdulazeez Yari kasa, domin ganin sun kwato jihar zamfara da Mutanen ta daga bautar dasu da Tsohon Gwamna Yari ya yi. A halin yanzu sun zo sun hada kai da Gwamna Matawalle domin ganin sun farfado da jama’ar Jihar Zamfara daga ragowar raunin cutar da Gwamnatin Yari ya bar musu.”
danfulani Gusau, ya kara da cewa, “Idan za’a tuna, lokacin da Matawalle ya karbi mulki, ya yi alkawarin cewa zai yi tafiya da duk wanda yakeson ci gaban Jihar, sai gashi ya cika alkawari inda yanzu a cikin Gwamnatin Bello Matawalle akwai mambobin Jam’iyyar APC wadanda suka hada da kwamishinoni da masu baiwa Gwamna shawara a bangarori da dama, ga kuma sauran Daraktoci da sauran masu rike da mukamai daban daban a fadin Jihar.”
Shugaban Jam’iyyar PDP na karamar hukumar Gusau ya ce, “A bayanin Gwamna Bello Matawalle lokacin da ya hau karagar mulki, ya ce, “yanzu Zamfara a hannun mu ta ke, domin haka ya rage namu mu gyarata ko mu karasa lalata ta, idan munaso mu gyarata ya zama dole mu ajiye duk wasu banbance-banbancen dake tsakaninmu domin farfado da Jihar baki daya daga gargadar da ta kusa fadawa ta hanyar koma baya wanda Gwamnatin da suka shude ta janyo.”
Shugaban Jam’iyyar PDP na karamar hukumar Gusau, Alhaji Tukur danfulani Gusay, ya bayyana Gwamna Bello Matawalle a matsayin Gwarzon Gwamna wanda tarihi ba zai taba mantawa da shi ba, musamman idan akayi la’akari da irin ayyukan ci gaba da gwamnan ya kawo ma Al’ummar Jihar Zamfara a shekara daya kacal da hawan sa bisa kujerar Gwamnan Jihar Zamfara.
danfulani Gusau ya kara da bayyana cewa,” Ko shakka babu duk mutumin da ya shigo Jihar Zamfara yanzu, yasan cewa an sami gagarumin zaman lafiya a duk fadin sassan Jihar baki daya, hakan ya faru ne a bisa Namijin kokarin da Mai girma Gwamna ya keyi, wanda kullum shi burinsa bai wuce ta yaya za’ayi a sami dauwamammen zaman lafiya a Jihar Zamfara, da kuma yadda ‘yan kasuwa da manyan kamfanonin kasashen waje zasu shigo domin ganin sun zuba jarinsu a Jihar, saboda yadda Allah ya hore ma Jihar Zamfara dimbin ma’adinai da arzikin kasa.” A cewarsa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: