Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home NAZARI

Shekara Daya Da Fara Fitowa: Gudumawar Jaridar NATIONAL ECONOMY Ga Tattalun Azikin Nijeriya

by Muhammad
February 21, 2021
in NAZARI
5 min read
National Economy
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Khalid Idris Doya,

A jiya Asabar ne jaridar NATIONAL ECONOMY ta cika shekara guda cif-cif da fara fitowa wacce ta himmatu wajen wallafa labarai, mukaloli, hirarki, da sharhi gami da shawarori kan lamarun da suka shafi tattalin arziki da alkinta lamarin tattalin arzikinn kasar nan.

Watanni kalilan da fara buga jaridar, Nijeriya da ma kasashen duniya suka tsinci kansu cikin annobar Korona wacce ta jawo mummunar baraka ga sashin tattalin arzikin duniya wacce ba a taba shiga irinsa a tarihi. Duk da wannan kalubale na Korona amma jaridar ta samu tabbatuwa da daurewa har zuwa yau da take bikin cika shekara guda. Ta samu cimma nasara zuwa yau ne sakamakon azama, himma, kwazo da jajircewar fitaccen mawallafinta, wato marigayi Samuel Ndanusa Isaiah, bisa ga kyakkyawar tsarin da ya ginata a kai.

Duk da mawuyancin halin da aka fuskanta a 2020, jaridar tattalin arziki ta National Economy ta samu tsayuwa bisa duga-duganta tare da tsayuwa kyam bisa manufa da matakin da mawallafinta ya samar da ita na tsage gaskiya da kuma kula da tattallin arzikin Nijeriya.

Mista Sam Nda-Isaiah, ya fada kan cewa karfin guiwarsa na dagewa kan fito da jaridar shine domin tabbatar da samar da yanayin da zai fitar da Nijeriya daga cikin tsaka mai wuya a bangaren tattalin arziki. Ya nuna cewa Nijeriya na bukatar a tallafota gami da saita akalar lamura, ya nuna gargadin cewa dole ne a yi gaggawa tallafo Nijeriya domin kareta daga fadawa cikin bala’i.

Bugu kuma da kari, shugaban, Sam Nda-Isaiah, ya nuna fatansa da begensa na ganin Nijeriya ta samu cimma nasarar daukaka da kaiwa zuwa matakin cigaban da suka dace gami da zama zakara a tsakanin kasashen duniya.

A kan haka ne, shugaban ya nuna matukar shawarar amfani da jaridar NATIONAL ECONOMY don zama jagora ga ‘yan Nijeriya a fannin cudanya da kasashen Afrika kan yarjejeniyar kasuwanci ta Africa Continental Free Trade Agreement (AfCFTA).

Don haka, Kashegarin ranar da zai rasu, Jagora Sam ya kafa hukumar masana tattalin arziki na jaridar NATIONAL ECONOMY. A ganawar da suka yi a wannan ranar, ya nuna bukatar cewa mambobin hukumar ya dace suke ganawa da yin zama duk bayan wata uku-uku domin samar da alkibla don tafi daidai da dukkanin masu ruwa da tsaki na AfCFTA.

Mambobin hukumar jaridar sun himmatu wajen yin aiki tare da hukumomin da suke da alaka gami da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da yin aiki tare wajen fitar da Nijeriya daga kakanikayin tattalin arziki da ake ciki, gami da bada shawarorin hanyoyin da za a bi wajen ganin tattalin arzikin Nijeriya ya samu gogayya da kasashen da suka cigaba tare da neman kaiwa zuwa matakin AfCFTA.

Mambobin hukumar gudanarwa na jaridar sun kunshi masana tattalin arziki da suka kunshi: Dakta Chuwunenye Kocha na jami’ar jihar Ribas, Fatakwal; kwararren mai bada shawara (Consultant) Dakta Emeka Okengwu; Farfesa Umma Abbas na jami’ar Bayero da ke Kano; mai bada shawara, Mista Abdulrauf Aliyu; shugaban rukunin jaridun LEADERSHIP Group Limited/NATIONAL ECONOMY Media Limited, LEADERSHIP A YAU, Mista Sam Nda-Isaiah; Farfesa Murtala Sagagi na jami’ar Bayero da ke Kano;  masanin tattalin arziki, Mista Ahmed Hussain Musa; Farfesa Lere Baale na makarantar Business School Netherlands International, Nigeria, da kuma Dakta Bongo Adi na Lagos Business School.

A halin da ake ciki, kuma abun farin ciki a nan shine, jaridar NATIONAL ECONOMY dai ta tsaya da kafafunta kyam, tare da tabbatar da cimma manufofi da muradin wanda ya kafata na ganin Nijeriya ta zama kasa wacce za a ke alfari da ita a duniyar nan. Domin kuwa hatta ma’aikatanta a shirye suke wajen ganin sun tafi da manufofin da aka samar da jaridan domin su, dukka don kishin kasa, bunkasar tattalin arziki da fatan kwarai wa Nijeriya.

 

 

Maharba Da Yadda Suke Bada Ta Su Gudunmawar Matsalar Tsaro

Daga Idris Aliyu Daudawa

Sana’ar harbi wata tsohuwa sana’ace wadda aka dade ko nace aka wayi wayi aka same ta tun daga Kaka da kuma Kakanni ko tun lokacin da ake cewa Bature Zaki, wanda yake wannan sana’ar sunan sa maharbi, hakanan ma kayayyakin da ake amfani da su wajen yin harbin, suma sun sha bamban. Akwai maharban da suke amfani da Bindiga wata irin ta toka wato ta gargajiya yayin da kuam wasu suna yin amfdani ne da Kwari da kuma Baka, kamar dai yadda kowa ya sai maharba suma sun sha bamban suna suka tara domin akwai wadanda suke daura fitila su shiga daji da dare su yi farauta mafarauta ke nan inda suke bidar namun daji wasu kananan wasu kuma manya, akwai kuma wadanda suke shiga daji sai sun kwashe wata daya, daga baya su dawo gida. Kananan maharban wasu za su dawo da yake hakan sukan kira kansu idan sun je irin wannan farautar su kan dawo da Zomo, Gada, da dai sauransu, amma manya sai su Bauna, da dai sauran wasu muggan namun daji wadanda dama ko su maharban da suka shahara sai  sun sha gashin Kuma.

Malam Ahmed Sale Soro dan aslin Jihar Bauchi ne ya kuma shafe shekaru fiye da talatin da biyu yana zaune a Jihar Nasarawa, ya kuma ce sun zo neman arziki ne, suka yi kuma sa’a al’ummar Jihar suka amshe su hannu bi- biyu. A halin da ake ciki yanzu shi ne kungiyar Maharba wadda aka fisani da suna Hunters ta Jihar Nasarawa, ya kuma ce suna tare da babban birnin tarayya Abuja. Yace suna tare da Shugabanni, Sarakuna dadai sauran mutane saboda kuma su taimaka masu, bama kamar wajen tabbatar da zaman lafiya ya kankama a Jihar Nasarawa, wannan kuma shi ne burin sun a farko. Bugu da kari kuam a matsayin sun a maharba komai dare komai rana, a shirye suke su taimakawa gwamnati da kuam duk wadanda suka nemi taimakon hakan.

Yadda kuma kungiyar take samun kudaden tafiyar da harkokinta ya bayyana cewa duk Unguwar data samu kanta cikin al’amuran ‘yan tayar da zaune tsaye, kjamar kananan barayi, da kuma ‘yan fashi da makami, suka fitini Unguwar su ake kira. Idan kuma sun je su taimaka masu cikin ikon Allah. Saboda suna sa’a su cimma nasara, ta haka sai su Barayi da sauarn ‘yan tada kayar baya su kauracewa zuwa wurin. Ta hakane suke samun kudaden da suke tafiyar da harkokin na kungiyar tasu, kamar taimakawa marayun yara wadanada aka kashe mahaifansu, lokacin da suke filin daga taimakama wasu   basu kuma samu dawowa da ran su ba, iyalan da suka bari haka ne ita kungiyar take taimaka masu. Ya kuma jadda cewa suna matukar cikin halin matsi na halin rayuwa.

Maganar suna kuwa samun tallafi daga gwamnati ya amasa cewa basu fara samu ba, saboda koda gwamnatin tana bayar da gudunmawar to su basu fara ganin wani ya kawoo masu ba. Domin kuwa itama gwamnatin tana bukatar taimako, kamar yadda suma suke bukata. Koda yake kamar yadda yai bayani sukan samu taimako daga wurin daidaikun mutanen da suka gaiyace su, su je su taimaka masu, ko su bi sojoji, ‘yansanda, DSS saboda duk ai suna hulda da su.

SendShareTweetShare
Previous Post

Bambancin ‘Web Da Internet’

Next Post

An Daure Dalibai Biyu Wata 18 A Gidan Yari Saboda Satar Na’urar Sadarwa A Jos

RelatedPosts

Mata

Yadda Mata Suke Jefa Yan’uwansu Mata Cikin Halaka ta Hanyar Tura Su Gidajen Aiki

by Muhammad
7 hours ago
0

A yayin da hukumomi suke ƙokarin suga sun magance safarar...

Jami’ar NOUN

Zamanin Farfesa Abdalla A Jami’ar NOUN

by Sulaiman Ibrahim
2 days ago
0

Daga Nasir S. Gwangwazo   Kamar yadda a shafin LEADERSHIP...

Watanni Biyu

Ayyukan Ta’addanci A Arewacin Nijeriya

by Sulaiman Ibrahim
6 days ago
0

Ga duk mai tabaraun hangen nesa, zai fahimci cewa lallai...

Next Post
Na'urar

An Daure Dalibai Biyu Wata 18 A Gidan Yari Saboda Satar Na’urar Sadarwa A Jos

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version