Wani mahimmin batu da ya kamata ace an yi bitarsa a shekarar da ta gabata ta 2020 shi ne bangaran shari’a wanda shima ya sha fama da fanfare, musamman wadanda suka samu kansu a komar ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro domin fuskantar hukuncin kuliya manta sabo.
Hakika wannan bangare shima ya taka mihimmiyar rawa a 2020 domin acikin wannan shekarar wata kotu da ke jihar Legas ta yankewa tsohon gwamnan jihar Abia Uzu Kalu hukuncin zaman gidan maza na shekara goma sha daya, ba a dauki lokaci ba kuma kotun kolin Najeriya ta warware wannan hukunci abinda har gobe ‘yan Najeriya da dama ke mamakin faruwar haka.
Kazalika a cikin shekarar 2020 ne mafiyawan gwamnoni suka tsallake siradin mulkin da suke kai, domin kuwa akwai wasu jahohin da ba za su manta da irin hukuncin da wasu kotuna suka gudanar ba na a cikin shekarar 2020.
Akwai misalin wannan a jihar Bayelsa da Imo da Kano da Katsina da kuma Sakwato da sauran wurare, wasu wuraran dai murnar suka yi harda shewa wasu kuwa kuka suka na bakin cikin abinda ya faru da su game da hukuncin da kotuna suka yanke.
Haka kuma idan muka koma akan batun rufe kan iyakokin Najeriya a shekarar 2020 ne gwamnatin Najeriya karkashin shugaba Muhammadu Buhari ta bada umarnin a duba yiwuwar bude kan iyakokin saboda wasu dalilai da gwamnatin da ta bayyana wanda har gobe ‘yan Najeriya na da shakku game da su.
Sai dai a maimakon murna da jin wannan labari na bude kan iyakokin Najeriya a wasu bangarorin na Najeriya musammna arewa abin ya zama tamtar ga koshi ga kwanan yinwa domin kan iyakoki hudu ne kawai aka bude sauran har gobe sunan garkame kamar gidan Yari.
Mutanen arewa wadanda sune suka fi kowa cin gajiyar bude kan iyakoki yanzu kuma sune suka fi kowa shan bakar wahala sakamakon rufe kan iyakokin da aka yi wanda ba a sa ranar bude su ba, batun da masana halayyar dan adam suke cewa lallai akwai nukufurci game da rufe bodojin Najeriya daga wannan gwamnati ta Buhari
Babu shakka mutanen jahohin Sakwato da Zamfara da Katsina da Jigawa suna cikin hali so sai, kuma abin ya fi kamari a cikin shekarar da ta gabata saboda yadda komi ya zama tamkar a kasar da ake yakin basasa.
Sannan jama’ar da ke wannan jahohi sun gamu da gamansu bayan da hukumar hana fasa kwabri ta kasa ta hana sayar da man fetur a cikin shekarar 2019, amma shekarar 2020 aka fi jin gashi game da wannan aika-aikata da salon karya wanda Allah ya rufawa asiri da gwamnatin Buhari ta yi.
Bana jin akwai wanda wannan bala’i bai taba ba, indai yana da alaka da garuruwa ko jahohin da ke makwabta da jamhuriyar Nijar kuma abin ya fi tsananta a shekarar 2020 saboda yanayin da aka shiga na gasawa jama’a aya a hannu da sunan hana shigowa da makamai daga kasar Libya da wasu ‘yan ta’ada ke yi kuma har gobe ba a daina shigowa da makaman ba, sannan kuma ba a bude kan iyakokin ba, ko saboda me oho!
Mutanen da suka rasa rayukansu da wanda suka suka sami manyan raunuka a sakamkon wannan garkame kan iyakoki, bincike ya nuna cewa na shekarar 2020 sun fi na kowace shekara yawa saboda yadda aka bada umarni akan mai uwa da wabi.
Hanyar dai sai da ta koma tamkar hanyar lahira don wanda zai bita bisa zabi biyu ne, idan Allah ya sauki shi lafiya haka ake so, idan kuma wani abu ya faru to daman anan tunanin haka, duk da cewa akwai jami’an tsaro a wannan hanya.
Bana jin akwai wani mutumin arewa da dan uwansa ko shi kansa da bai auna arizki ba a shekarar da ta gabata ta 2020 akan hanyar Abuja zuwa Kaduna daga barazanar masu dauke jama’a sai an biya kudi ba, kuma har gobe wannan danyen aikin na cigaba da faruwa sai dai a samu sauki yau gobe a koma.
Lallai idan da za a bada wata gagarumar kyauta a shekarar 2020 ina iya bada shawara a baiwa hanyar Abuja saboda kaurin suna da sanwantar da ran dan arewa kai har da ma duk wanda yanayi ko tsautsayi ya biyo da shi wannan hanya.
Akan batun yadda ta lalace da kuma gyaran da ake yi wa wannan hanya, shi kan shi abin a zo a gani ne, domin a bisa wannan yanayi da ake mutane da dama sun mutu wasu sun jin raunuka da dai sauransu.
Wani batu da yakamata ace na dan tabo shi ne irin yadda malaman addinin Musulunci jikin su ya yi sanyi a shekarar 2020 ina nufin malamai wadanda suka yi kokarin wajan ganin an zabi shugaba Muhammadu Buhari ya dare kan mulki, hakika abubuwan da suka biyo baya a shekarar 2020 abin takaici ne.
Malamai sun ga tasko, sun ji jafa’I sun ga abinda ba su yi tunani ba, sun kuma rasa abinda za su ce akan yadda suka taimaka wajan kawo wannan gwamnati yanzu kuma ga halin da aka shiga amma an ji sun yi shiru kamar an aiki Bawa garinsu.
Babu shakka, shekarar 2020 ba zata taba gushewa a zukatan Malamai ba amma wadanda suka yi uwa makarbiya wajan ganin an kawo gwamnatin shugaban Buhari wanda ba su sa baki ba, kuwa shekarra 2020 ta zame masu tamkar wadanda suka sauke farali saboda kila sun hango cewa za a samu matsala a wannan tafiya.
Komi ke nan, yanzu dai an fita daga wancan bakar shekara da take da munanan abubuwa wanda kuma har gobe neman tsari ake daga Allah kadda ya maimaita abinda ya faru a cikinta ga wadannan bayi nasa masu laifi kuma masu tuba a kodayaushe.
Anan zan tsaya da wannan rubutu nawa wanda ya kwashe sati uku ina yin sa, saboda haka ina mika sakon sabuwar shekara ga dinbin masu karatun wannan jarida ta Leadership Ayau da kuma wannan shafi nawa na Mukalla Laraba musamman wadanda suke aiko mani da sakon waya da kuma kira domin bada shawara da kuma karfafawa. Na gode, sai wani satin idan Allah Ya kaimu da rai da lafiya.