‘Yan’uwa Musulmi assalamu alaikum wa rahmtullahi ta’ala wa barkatuh. Da yake wannan watan da muka shiga daya ne daga cikin watannin aikin Hajji, za mu mayar da hankali a kan bayanin aikin Hajji zuwa abin da ya sauwaka kafin mu ci gaba da darasin da muke yi a kan tarihin Manzon Allah (SAW) cikin yardar Allah.
Aikin Hajji ibada ne da yake da lokaci kebantacce da wuri kebantacce da ake gudanarwa. Ma’ana ba a ko wane lokaci ko wurin da mutum ya ga dama ne ba zai ce zai yi Hajji. Akwai lokaci da wurin da Allah ya kebance su da Hajjin.
Lokaci (na zamani) da ake Hajji shi ne wata guda uku, Shawwal, Zhul-kiyda, Zhul-hajji, su ne kuma ake kira da Mikati zamani. Allah (SWT) ya ce a cikin Alkur’ani: “Suna tambayar ka game da wadannan jirajiran wata, ka ce lokuta ne na mutane da suke ibadodinsu.” Don haka da zarar watan Shawwal ya kama, to an shiga lokacin da mutum zai iya yin harama da Hajji.
A wurin mu Malikawa, mun dauki watannin nan guda uku a matsayin lokacin Hajji, wasu kuma sun ce a’a, daga kwana goman farkon nan na Zhul-hijja, lokacin ya kare, to amma kuma idan aka yi la’akari za a ga cewa akwai sauran ibadodin Hajjin da suka shige wadannan kwanakin goma irin su Jifa da ake dawowa Mina a yi bayan Sallar Idi da Dawafin bankwana. Shi ya sa Malikawa muka dauki watannin ukun baki daya a matsayin lokacin Hajji. Kuma Ibn Hazan ya goyi bayan haka, don ba za a dauki wata biyu da kwana goma a ce musu watanni uku ba.
Kamar yadda bayani ya gabata, Hajji ba a ko ina ake daura haramar yin sa ba, yana da wuraren da Shari’a ta kebance don yin harama da shi. Duk wanda zai yi Hajji ko Umura, bai halasta gare shi ya tsallaka wadannan wuraren ba tare da ya yi harama ba.
Manzon Allah (SAW) ya sanya wa ko wadanne mutane wurin da za su yi harama (Mikati). Ya sanya wa mutanen Madina Zhal-hulaifa ya zama wurin haramarsu. A yanzu ana kiran wurin da sunan Abaru Ali. Haka nan sauran mutanen duniya da suka fara wucewa Madina ziyarar Annabi (SAW) daga ko ina a duniya, idan za su dawo Makka yin Hajji ko Umura su ma a nan Zhal-hulaifa za su yi harama. Ba za su ce sai sun koma Mikatinsu ba da aka sanya musu. Wurin yana nan daga Arewacin Madina kuma tsakaninsa da Makka tafiyar kilomita 450 ne, kusan shi ne mafi tsawo daga Makka a cikin sauran wuraren haramar Hajji.
Annabi (SAW) ya kafa wa mutanen Sham (Siriya) da sauran kasashe irin su Palasdin da Urdun wurin da ake kira Juhufa ya zama wurin haramarsu. Wurin yana nan a arewa-maso-yammacin Makka kusa da Radiga wadda Hausawa suke kira da Radinga. Tsakaninsa da Makka tafiyar kilomita 187. Amma tunda ruwa ya shafe Juhufa a halin yanzu, Radiga ce ta zama wurin haramar su mutanen Sham da Misra da sauran wadanda suka bi ta wajen, ita kuma tsakaninta da Makka tafiyar kilomita 204. Muma mutanen Nijeriya nan ne Mikatinmu da sauran mutanen kasashen da za su bi wurin, kamar na Yammacin Afirka.
Su kuma mutanen Najadu, Annabi (SAW) ya sanya musu Karnul-manazil ya zama Mikatinsu. Wani dutse ne da ke gabashin Makka yana kallon Arfa. Tsakaninsa da Makka tafiyar kilomita 94.
Su kuwa mutanen Yemen, Annabi (SAW) ya sanya wa mutanensu Yalamlam ya zama Mikatinsu. Shi ma dutse ne da ke kudancin Makka. Tsakaninsa da Makka tafiyar kilomita 54.
Annabi (SAW) ya kafa wa mutanen Iraki Zatu’irkin a matsayin Mikatinsu. Wuri ne da yake arewa-maso-gabas din Makka. Tsakaninsa da Makka tafiyar kilomita 94, nisan shi da Makka daya ne da na Mikatin mutanen Najadu.
Wadannan wurare da Annabi (SAW) ya kafa, su ne wuraren da mutanen duniya za su yi haramar Hajji ko Umura.
Idan zuwa Hajji ko Umura ya kama mutum a wata kasar da ba tashi ba, zai yi amfani ne da Mikatin da mutanen wannan kasar suke yin harama, ba zai ce tunda shi ba dan kasar ne ba, sai ya koma ta Mikatin kasarsa, a’a, zai yi haramar ce a Mikatin ‘yan kasan, ma’ana kamar shi ma ya zama dan kasar ke nan.
Amma su kuma wadanda suke cikin Makka (baki da ‘yan garin), a nan cikin garin ne za su yi harama. Kamar misali wadanda suke Hajjin Tamattu’i, bayan sun kammala Umura, to idan ranar da za a yi haramar Hajji ta zo, tun daga gida za su yi harama ba sai sun je wani wuri ba.
Amma idan dan cikin Makka zai yi Umura bayan Hajji, sai ya fita zuwa Tan’im kafin ya yi harama kamar yadda Annabi (SAW) ya yi umurni a kai Ummul-Mu’umina Aisha (RA) ta yi haramar Umura.
Tambihi
Batun Mikatin da maniyyatanmu na Nijeriya suke tsallakawa har sai sun je Jidda kafin su yi haramar Hajji ko Umura abu ne da yake bukatar gyara a kai.
Juhufa, Mikatin mutanen Sham shi ne Mikatin mu ‘Yan Nijeriya, amma saboda ruwa ya shafe shi sai Mikatin ya koma Radinga.
Idan mutum ta mota zai je, dole ta Madina zai bi domin ruwa ya riga ya kafce Juhufa. Don haka a can Mikatin Madina mutum zai dau harama. Duk da cewa Radinga tana gaban Zhal-hulaifa, baki dayan maniyyatan da suka fito daga Madina a nan za su yi harama, ba za su ce su bari sai sun je Radinga da yake gaba ba. Idan mutum ya yi haka, ya aikata sabo kuma sai ya ba da jini kamar yadda jamhurun Malamai suka fada. Imamun Nawawi ya kore cewa akwai sabani game da wanda ya yi hakan zai ba da jini ko a’a, ya tabbatar da cewa sai an ba da jinin. Ya yi bayanin haka a cikin Sharhinsa na Muslim da Muhazzabu.
Shehun Musulunci, Shehu Ibrahim Dan Alhaji Abdullahi Kaulakha (RA), a cikin littafinsa na Manasikul Hajji ya fadi cewa “duk wanda ya tsallake Mikati zai ba da jini.”
Dangane da hukuncin wanda aka wuce da shi ta jirgin sama ba a tsaya yin harama a Mikati ba, Shehun ya fada a cikin littafin cewa “Matafiya a cikin jirgin sama, ya fi dacewa su yi harama na Hajji ko Umura a karshen filin jirgin da za su tashi zuwa Jidda tun kafin su zo Mikatin.”
Ya dogara ne kuma da fassarar da Sahabban Annabi (SAW), Aliyu bin Abi Dalib (Allah ya girmama fuskarsa) da Abdullahi bin Umar (RA) suka yi wa ayar “ku cika Hajji da Umura don Allah.”, ma’anar cikawar in ji Sahabban ita ce yin harama daga gida ko wurin da mutum zai taso.
Ibrahimun Naka’i (RA) ya ruwaito cewa Sahabbai sun so ga wanda bai taba yin Hajji ba idan zai yi Hajjinsa na farko; to ya yi harama tun daga gida.
A cikin Ma’alimus Sunani (Sharhi Abi Dawuda), wurin Hadisin Mikati, ya fadi cewa “Ma’anar fadar kafa wurare da Annabi (SAW) ya yi na wadannan Mikati ita ce kar mutum ya tsallaka ba tare da ya yi niyya da harama ba.” Dukkansu sun hadu a bisa cewa idan mutum ya yi harama kafin Mikati, ya isan ma sa (Hajjinsa lafiya kalau), domin ba kamar Mikatin Sallah ba ne da ba a yarda a yi ba sai a lokacin da aka sanya.
Har ila yau, a cikin Sharhin Mugni, Dan Kudamata ya ce “Babu sabani kan cewa duk wanda ya yi harama da Hajji ko Umura kafin Mikati, haramarsa ta yi, duk hukuncin harama ya hau kansa.”
Ibn Munzul ya ce “dukkan Malamai sun hadu a kan cewa duk wanda ya yi harama kafin Mikati, ya zama mai harama (haramarsa ta yi), sai dai an fi so mutum ya yi a wurin Mikati”.
Shi kuwa Buha Isa ya ce “abin da ya fi shi ne alhazai su yi harama tun daga garinsu”.
Malamai irin su Alkamatu, Aswadu, Abdulrahman, da Abu Is’haka sun kasance suna yin harama daga gidansu bisa kafa hujja da abin da Uwar Muminai Ummus Salma (RA) ta ruwaito cewa, ta ji Manzon Allah (SAW) yana cewa “Duk wanda ya yi harama da Hajji ko Umura daga Masallacin Baitul Makdisi zuwa Masallacin Allah Mai Alfarma, an gafarta ma sa zunubinsa na abin da ya gabata da wanda ya jinkirta ko kuma Aljanna ta wajaba gare shi.” Abu Dawuda ya ruwaito Hadisin.
A lafazin da Ibn Majah ya ruwaito kuma, Hadisin ya ce “Duk wanda ya yi harama da Umura daga Baitul Makdisi ya taho Makka, an gafarta ma sa zunubinsa.”
Sayyidina Abdullahi bin Umar (RA) ya yi harama da Hajji tun daga Iyliya’a (Baitul Makdis).
Haka nan, Nisa’i da Abu Dawuda sun ruwaito daga Baddi bin Ma’abadi cewa shi (Baddi) ya yi harama daga nan (Baitul Makdis), sai Abdullahi bin Umar (RA) ya ce ma sa “Ka dace da Sunnar Annabinka (SAW)”.
Duk wadannan karatuttuka suna bayani ne a kan yin harama kafin zuwa Mikati.
Bisa duk wadannan hujjojin da suka gabata, sai Shehu Ibrahim (RA) ya ce, “Tun daga zamanin Sahabbai har zuwa yau, a fili yake cewa yin harama kafin Mikati shi ya fi a kan mutum ya wuce Mikatin ba tare da harama ba.”
Mu Nijeriya da sauran wasu kasashen da Mikatinmu ya zo daya, babu filin jirgi a Radinga, don haka kai tsaye ake wucewa Jidda kuma hakan ya sa an keta Mikati ba a yi harama ba.
Wasu kasashen, kamar su Misra da Sudan duk za ka ga maniyyatansu sun shiga jirgi da haraminsu. Idan aka zo wurin da Mikati yake, sai a cikin jirgin a sanar da su cewa kowa ya yi niyya.
Muma ya kamata a rika yi wa maniyyatanmu haka. Idan kuma direbobin jirgin ba su san Mikatin ba balle su sanar, sai a duba a ga wane filin jirgi ne na karshe wanda idan aka tashi daga shi ba za a sauka a ko ina ba sai Jidda (kamar Khurduum kenan), sai a yi haramar a can.
Saboda shi Mikati ba a wuce shi, galibin malamai sun ce duk wanda ya wuce Mikati bai yi harama ba ya wajaba ya yi yanka tare da Istigfari, wasu ma sun ce matukar mutum ya wuce Mikati bai yi harama ba to Hajjinsa sai dai ya bari zuwa shekara mai zuwa ya dawo.
Sun fadi haka ne saboda Hadisin Abdullahi bin Umar (RA) da ya ce “Manzon Allah (SAW) ya farlanta Mikati.” Ma’ana tilas ne mutum ya yi harama a nan saboda ya zo da lafazin “Yahillu” watau “Ya yi harama a nan”. Shi labari ne da ya zo da ma’anar horo, inda horo ne ya zo da ma’anar labari sai a ce yana karfafa wajibci ne.
Wasu Malamai suka ce idan mutum ya wuce Mikati sai kuma ya sake komawa daga baya ya daura harami a can (Mikatin), shi kenan ba zai ba da jinin nan ba. Wasu kuma suka ce ko da mutum ya koma sai ya ba da jinin.
An yarda cewa za a iya yin harama kafin a zo Mikati, amma ba a yarda a wuce Mikati ba tare da an yi harama ba.
Wata rana na tambayi wasu manyan malamai uku a Jidda kan cewa mene ne ya sa muke yin harama a Jidda, alhali masana sun san cewa Jidda ba Mikatinmu ba ce? Suka ce gaskiya ne lallai Jidda ba Mikatinmu ba ce, Mikatinmu yana cikin ruwa, sai dai kawai lalura ce take sawa a yi hakan.
Amma kuma wasu Malamai sun yi bayanin cewa a batun Mikati babu zancen lalura, domin duk abin da Shari’a ta baiwa mutum kofa a kai, babu zancen lalura.
Annabi (SAW) ya ce mutum zai iya daukan haramar Hajji daga can Sham wajen kabarin Annabi Ibrahim (AS), duk kuwa da cewa akwai Mikatin da aka sanya wa mutanen kasar. Bisa fahimtar Malamai, wannan yana nuni da cewa mutum zai iya daukan harama tun daga gidansa.
Saboda haka tun da Shari’a ta ba da mafita, bai kamata a rika shige Mikati ba tare da an yi harama ba. Malaman da suka saukaka ne suka ce idan mutum ya yi hakan, dole sai ya yi hadaya, wasu kuma suka ce sai dai mutum ya dawo wata shekarar ya sake yin harama.
Don Allah muna kira ga mahukuntanmu na Aikin Hajji su gyara wannan. Domin babu wani Mashahurin Malami da ya taba cewa ya inganta a wuce Mikati ba tare da an yi harama ba.