Kyaftin din tawagar Super Eagles ta Nijeriya kuma dan wasan da yafi buga wa kasar wasanni a tarihi Ahmed Musa na ci gaba da taka rawar gani a wasannin da yake bugawa tun bayan komawarsa tsohuwar kungiyarshi ta Kano Pillars a watan jiya, Musa ya dade bai buga wa Nijeriya wasa ba duk da cewa shi ne kyaftin din tawagar a halin yanzu sakamakon rashin kungiya na tsawon lokaci.
A gasar cin kofin nahiyoyi da hukumar kwallon kafa ta FIFA ta shirya a shekarar 2013 Musa ya fara buga wa Nijeriya kwallo, inda ya buga dukkan wasannin guda uku da Nijeriya ta buga a gasar yayin da aka fitar da su tun a matakin rukuni.
Bayan buga dukkan wasannin share fage, an saka sunan Musa a cikin tawagar Nijeriya wadda Stephen Keshi ke jagoranta a wancan lokaci domin buga gasar cin kofin duniya na shekarar 2014, Musa ya zura kwallaye biyu a wasan karshe na rukunin F inda Nijeriya ta yi rashin nasara da ci 3–2 a hannun kasar Argentina.
A watan Oktobar shekarar 2015, bayan ritayar Bincent Enyeama daga buga kwallon kafa, kocin Nijeriya, Sunday Oliseh ya nada Musa a matsayin kyaftin din tawagar sai dai an sauya wannan shawarar a shekarar 2016 yayin da aka nada Mikel John Obi a matsayin kyaftin din tawagar Nijeriya Musa kuma ya koma matsayin mataimakin Kyaftin.
A watan Mayun 2018 an saka shi cikin jerin ‘yan wasa 30 na farko da za su wakilci Nijeriya a gasar cin kofin duniya ta FIFA 2018 a kasar Rasha, Musa ya matukar taka rawar gani a wasansu da kasar Iceland inda ya jefa kwallo biyu a ragar turawan, amma hakan bai hana Nijeriya ficewa daga gasar ba sakamakon rashin nasara da suka yi a hannun Argentina.
A watan Yunin shekarar 2019 Musa ya zama dan wasa na uku da ya fi taka leda a tarihin tawagar Super Eagles inda ya zarce Nwankwo Kanu, Musa ya zama dan Nijeriya na farko da ya ci fiye da kwallo daya a gasar cin kofin duniya ta FIFA, bayan ya zura kwallaye biyu a ragar Argentina a gasar cin kofin duniya ta FIFA ta 2014.
Musa kuma shi ne dan Nijeriya na farko da ya zura kwallo a gasar cin kofin duniya ta FIFA guda biyu, bayan ya zura kwallaye biyu a ragar Iceland a matakin rukuni na gasar cin kofin duniya ta FIFA 2018, jimilla ya buga wasanni 108, shi ne dan wasan da ya fi buga wa Nijeriya wasa a tarihi.
Wasan karshe da Musa ya buga wa Nijeriya shi ne wanda ya shigo a minti na 94 a fafatawar neman buga gasar kasashen nahiyar Afirika a tsakaninsu da Guinea Bissau ranar 27 ga watan Maris na shekarar 2023,amma ya na cikin ‘yan wasan da suka wakilci Nijeriya a gasar kasashen nahiyar Afirika da aka buga a kasar Kwaddibowa inda aka doke Nijeriya a wasan karshe da ci 1-0,duk da cewar Musa bai buga wasa ko daya ba har aka kammala gasar ya matukar taimaka wa ‘yan wasan Nijeriya da shawarwarin irin nasu na tsoffin kanu a harkar kwallon kafa.
Tun bayan dawowarshi Kano Pillars da take leda Musa ya zura kwallaye uku ya taimaka aka zura biyu a wasanni 4 da ya bugawa Sai Masu Gida, hakan ya sa ake tunanin ya dawo da rigarshi ta tawagar Nijeriya da ya rasa na tsawon lokaci idan ya ci gaba da taka rawar gani.