Tare da Bakir Muhammad
Bitcoin wani tsarin kudi ne da ake amfani da shi a intanet kadai, kuma yana amfani a duk duniya ta hanya bai daya, kuma babu wani banki guda daya da yake kula da wannan nau’in kudin, wani masanin fasaha mai suna Satoshi Nakamoto ne ya kirkiro fasahar Bitcoin a shekarar 2009, kuma masu ta’ammuli da nau’in kudin sun a yi a tsakanin su ba tare da wani mutum na uku ba wanda zai lura da ta’ammulin tsarin sakar sama na intanet ne kawai ke kulla ta’ammulin.
Ana yin amfani da kudin Bitcoin wajen musanyar kudade a sahar intanet, ana iya siyan hajoji ma, a shekarar 2015 kadai ‘yan kasuwa kimanin 100,000 ne suka yi mu’amala da kudin Bitcoin, ana iya amfani da kudin na Bitcoin domin zuba hannun jari a wasu kamfanoni, a wani bincike da jami’ar Cambridge ta gudanar a shekarar 2017 ta gano akwai akalla kusan mutum sama da miliyan biyar da suke amfani da kudin na Bitcoin.
Ta Ya Ya Wannan Na’uin Kudin Yake Aiki?
Ya Ake Samun Kudin To?
Akwai hanyoyi da yawa na samun wannan nau’in kudin, misali na farko shine ana siya ta sahar intanet, akwai shafukka na sahar intanet da suke siyar da nau’in kudin, mutum zai shiga shafin sai ya zabi yawan Bitcoin da yake bukata sai a cire kudi a take daga akant din shin a banki, a take kuma za’a sa mishi wannan adadin na Bitcoin a jikar ajiyarshi ta intanet wato (Wallet), ana iya samun Bitcoin a shafukkan wasanni na intanet (Online games) in mutum ya buga wasa ya yi bijinta sai a bashi kyautar Bitcoin in da zai daura bayanin jikar ajiyarshi a take Bitcoin zai shiga jikar tashi, da kuma wasu hanyoyin amma wadannan su suka fi shahara.
Ya Yanayin Darajar Kudin Yake?
Kudin ya na da daraja sosan gaske, kudin ya ninka zinare daraja sau bakwai, ya ninka dalar Amurka daraja sau goma sha takwas, masu buga caca a sahar intanet ne su ke sa darajar kudin yak e hauhawa ko wanne lokaci, an fi amfani da shi a kasashen Amurka da Kanada da kusan duk kasashen turai, da kasar Sin da kasar Jafan.
Shin Ba Matsalar Tsaro Wajen Amfani Da Kudin?
Shi dai ba kamar kudin takarda bane, babu yadda za ayi barayi su sace shi ko masu kutse su kutsa su gano lambar katin banki su yi sata a akant din ajiya, shi abu ne da ya ke amfani da adireshin mutum wanda shi kadai ya san abun shi, abu daya aka fi tsoro wajen amfani da kudin, samun mazambata da ka iya siyar wa mutum kayan bogi sai a tura musu wannan kudin, ko kuma su siyar wa mutum Bitcoin ya biya su da kudin takarda amma su ki tura mishi Bitcoin din cikin jikar ajiyar shi ta intanet.
A yanzu ana kara samun masu amfani da kudin Bitcoin misali kamfanin hada-hadar kudi na intanet wato PayPal wanda yake kasar Amurka ya na amsar kudin na bitcoin, haka kamfanin Microsoft ma mai kera wayoyi da kwamfutoci da manhajjojin kwamfuta (Softwares) da kamfanin Dell shi mai kera kwamfuta da wani kamfani mai suna Newegg.