Shin Kun San Wasu Lamuran Shugaba Xi Jinping Game Da Jihar Xinjiang?

Xianjing

Daga Zainab Zhang,

Shugaban kasar Sin Xi Jinping yana kaunar jihar Xinjiang, inda ya kai ziyara da ganin abubuwan dake gudana a jihar, da halartar taron tattaunawa na tawagar wakilan jihar, da shugabanci taro don tattauna shirin raya kasa da yin kwaskwarima kan jihar, da amsa wasikar da ’yar malam Kurban Tulum ta rubuta masa da sauransu.

Yadda ake alfahari da zama dan jihar Xinjiang

A watan Afrilu na shekarar 2014, shugaba Xi Jinping ya kai ziyara jihar Xinjiang don gane ma idonsa abubuwan dake faruwa, inda ya ziyarci kamfanin samar da ’ya’yan itatuwa na Xinjiang dake birnin Urumqi.

A dakin baje kayan kamfanin, ana iya ganin busassun ’ya’yan itatuwa iri iri, Xi Jinping ya kalla tare da kuma sauraran bayanai game da kayayyakin, inda ya yaba yadda aka adana wasu nau’in busassun ’ya’yan itatuwa mai suna Xing da Zao masu dadin ci. Ya dauki wani busasshen inabi ya kuma tambaya, “Ko ba a yi amfani da takin zamani?” Yayin da ya ga yadda ake sayar da kowace jakar dabinon Hotan kan farashin Yuan 190, sai shugaba Xi ya tambaya, kan “Nawa jama’a suke samu daga cikin wannan?” Daga baya kuma, ya kara yin wasu tambayoyi kamar “Kuna da tambarin kayanku?”, “Yaya za a gano fifikon kayan ’ya’yan itatuwa na jihar Xinjiang, saboda sun yi kama da na yankin tsakiyar Asiya?” da sauransu.

A yayin taron tattaunawa da aka gudanar a yayin ziyarar da ya kai, shugaba Xi Jinping ya tuna da labarinsa lokacin da ya shiga tawagar soja a shekaru 60 zuwa 70 na karnin da ya gabata, ya ce, a lokacin yana yankin arewacin lardin Shan’anxi, yana begen zuwa jihar Xinjiang. Akwai burodin Nang, da shinkafan da aka ci da hannu, da tsiren naman rago da sauransu, babu shakka abin alfahari ne zama dan jihar Xinjiang.

Kan mu a hade yake kamar ’ya’yan rumman

A yayin taron tattauna daftarin zama na biyar na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 12 na tawagar wakilan jihar Xinjiang a watan Maris na shekarar 2017, wani wakili daga yankin, ya mikawa Xi Jinping hoton iyalan malam Kurban Tulum.

Iyalin dake zaman jin dadi.

Mene ne labarin Xi Jinping da iyalin?

Dattijo Kurban wani manomi ne dake garin Yutian na jihar Xinjiang. Yau fiye da shekaru 60 da suka gabata, don nuna godiya ga samun ’yancin jihar, ya tashi daga garinsa gundumar Yutian ta jihar Xinjiang ya hau jaki ya sha kilomita kusan 4000 ya zo birnin Beijing don nuna gaisuwa ga marigayi shugaban kasar Sin Mao Zedong, daga baya shugaba Mao ya taba ganawa da shi sau biyu.

A watan Janairu na shekarar 2017, shugaba Xi Jinping ya rubuta wa ’yar marigayi Kurban wasika, inda yake fatan dukkan iyalin za su yi koyi da marigayi Kurban, tare da zama abin misali na kaunar jam’iyyar kwaminis ta Sin, da kasar Sin, da al’ummar kasar Sin, da sa kaimi ga jama’ar kabilu daban daban da su hada kai kamar ’ya’yan rumman, don samar da kyakkyawar makoma a jihar Xinjiang a karkashin jagorancin jam’iyyar kwaminis ta Sin.

Wannan mataki yana da kyau

Yadda ake aiwatar da manufofin jam’iyyar kwaminis ta Sin dake shafar addinai a jihar Xinjiang, shi ne batun da Xi Jinping yake yin tunani a kai.

A watan Afrilu na shekarar 2014, a kauyen Ayageman dake garin Turizak na jihar Xinjiang, yayin da Xi Jinping ya gano cewa, Tursun Malaiti shi ne Liman masallacin kauyen, sai ya ziyarce shi don kara fahimtar yadda ake abubuwa ke gudana a masallacin gami da harkokin addini a kauyen.

Tursun ya bayyanawa shugaba Xi Jinping cewa, yayin da yake tafsiri game da ayoyin alkur’ani, ya kan kuma yi bayani game da manufofin jam’iyyar, ta yadda jama’ar kauyen za su kara fahimtar manufofin.

Xi Jinping ya ce, wannan mataki yana da kyau, ya kamata a maida harkokin addini bisa yanayin zamantakewar al’umma mai tsarin gurguzu, da gayawa jama’a tunanin raya zamantakewar al’umma mai tsarin gurguzu, ta hakan jama’a za su yi rayuwa mai dadi.

Xi Jinping ya dora muhimmanci ga ayyukan addini, yana ganin cewa, aiki mafi muhimmanci ga jama’ar jihar Xinjiang shi ne hadin kan kabilu da kuma girmama addinai.

Yadda jama’ar jihar za su kara jin dadin zaman rayuwa

Xi Jinping ya kiyaye maida hankali ga kauyen Daxi dake jihar Xinjiang.

A watan Yuni na shekarar 2009, Xi Jinping ya ziyarci kauyen Daxi tare da yin bincike game da ayyukan raya jam’iyyar kwaminis ta Sin. A watan Afrilu na shekarar 2014, Xi Jinping ya ambaci kauyen Daxi a yayin da ya ziyarci jihar Xinjiang. A watan Satumba na shekarar 2014, Xi Jinping ya aikawa sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminis na kauyen Daxi da mazaunan kauyen wasika cewa, yana mayar da hankali a kansu da kuma kauyen

A cikin wasikar, Xi Jinping ya yi nuni da cewa, bunkasuwa da babban sauyin da kauyen Daxi ya samu, ya shaida cewa, an aiwatar da manufofin jam’iyyar masu kyau, da kuma yadda jama’a daga kabilu daban daban suka yi kokari tare, ta yadda jama’a za su ji dadin zaman rayuwarsu.

Game da shirin raya jihar Xinjiang da aka tsara a wadannan shekaru, an gudanar da taron kwamitin tsakiya na jam’ iyyar kwaminis karo na uku daga ranar 25 zuwa 26 ga watan Satumba na shekarar 2020 a birnin Beijing, don tattauna ayyukan jihar Xinjiang, inda Xi Jinping ya halarci taron tare da gabatar da muhimmin jawabi.

Xi Jinping ya jadadda cewa, a halin yanzu da kuma nan gaba, ya kamata a martaba manufofin tafiyar da harkokin jihar Xinjiang na jam’iyyar a sabon zamani, da kokarin raya jihar mai hadin kai, da wadata, da ci gaban al’adu, da jin zaman rayuwa, da kuma kiyaye muhalli bisa tsarin gurguzu mai sigar kasar Sin ta musamman.

Xi Jinping ya jaddada cewa, tun zamanin dauri, akwai kabilu daban daban a jihar Xinjiang, kuma dukkansu al’ummar kasar Sin ne. Ya kamata a tsaya tsayin daka kan manufar maida addinin Musulunci bisa yanayin kasar Sin don cimma burin raya addini yadda ya kamata.

Jihar Xinjiang da kasar Nijeriya dukkansu suna da musulmai masu tarin yawa, don haka harkokin addini da yadda musulmai ke rayuwa a jihar Xinjiang, sun jawo hankalin musulmai dake kasar Nijeriya sosai. Idan aka samu wasu labarun dake shafar musulmai a jihar Xinjiang, to, hankalin musulmai a kasar Nijeriya na karkata gare su. Shi ma shugaba Xi Jinping yana kula da zaman rayuwar musulmai. A yayin da yake ziyara a jihar Xinjiang a shekarar 2014, Xi Jinping ya ziyarci masallacin Yanghang dake birnin Urumqi, hedkwatar jihar tare da tattaunawa da malaman addini na jihar Xinjiang, inda Xi ya bayana fatan mabiya addinai za su martaba akidar kaunar kasa da ta jama’a, da yaki da masu tsattsauran ra’ayin addini, da jagorantar mabiya addini da su fahimci ka’idojin addini, ta hakan zai taimaka wajen bunkasa tattalin arziki da kyautata zaman rayuwarsu.

Asilihan Nazha’erhan, dan kabilar Kazakh ne dake zaune a jihar Xinjiang ta kasar Sin, shekarunsa ya kai 56 da haihuwa, ya kuma zama Liman masallacin Hongdun dake birnin Altay na jihar har tsawon shekaru 25. Ya yi bayani cewa, idan musulmai sun yi aure, bayan da suka yi rajista a hukumomin harkokin jama’a ta gwamnatin, za su gayyace shi gidansu don na tabbatar da auren. Idan kuma wani ya mutu, zai je cibiyar samar da hidima ga iyalan mamaci bisa addini, don a binne gawar. A jihar Xinjiang, gwamnati ta kare ayyukan addini bisa doka, da kuma girmama al’adun gargajiya na musulmai.

Abuduwaili Abulimiti shi ne shugaban kungiyar addini musulunci ta garin Shache dake yankin Kashgar na jihar kuma limanin masallacin Altun dake garin Shache. Masallacin Altun yana da dogon tarihi na shekaru fiye da 480, kuma musulmai 300 suna iya yin sallah a lokaci guda. Kamar sauran masallatai, wannan masallaci yana da takardun iznin yin amfani da kasa, da iznin yin amfani da gine-gine, da iznin wurin yin ayyukan addini da hukumomin gwamnati da abin ya shafa suka bayar, don haka, ana tabbatar da moriyarsa bisa doka. A shekarar 2006, an maida shi a matsayin wurin tarihi da Sin ta fi ba shi kariya, kana Sin ta bada kudin musamman don gyara shi.

Mataimakin shugaban kungiyar addinin musulunci ta yankin Ili na jihar Xinjiang kuma Liman masallacin Shan’anxi Da na birnin Yining Ma Jirong ya bayyana cewa, musulmai daga kabilu daban daban na jihar suna iya koyon ilmin addini ta hanyoyi daban daban cikin sauri, wadanda suka biya bukatun musulmai na koyon ilmin addini.

Wannan ya shaida cewa, jam’iyyar kwaminis ta Sin da gwamnatin kasar Sin suna girmama tare da kula da yadda musulmai a jihar Xinjiang suke rayuwa.

A ranar 13 ga watan Afrilu na bana ne, musulmai a sassam duniya suka fara Azumin watan Ramadan. Kamar sauran takwarorinsu musulmai dake sassan duniya, musulmai fiye da miliyan 22 dake kasar Sin ciki har da na jihar Xinjiang, su ma sun fara azumi har na tsawon wata guda bisa ka’idojin addinin musulunci. Kamar yadda suke yi a kowace shekara, ana yin salloli sau biyar a kowace rana a masallatar fiye da 34,000 dake sassa daban-daban na kasar Sin, musulmai suna zuwa masallatai don yin sallah da sauran Ibadu a kan lokaci, da kuma yin azumin watan Ramadan har na tsawon wata guda. Bayan da aka kafa sabuwar kasar Sin, gwamnatin kasar Sin tana martaba yadda musulmai suke azumi a watan Ramadan. Ana kare moriyar musulmai bisa tsarin mulkin kasa da dokokin kasar.

Xi Jinping ya yi nuni da cewa, burin farko na jam’iyyar kwaminis ta Sin shi ne samun rayuwa mai dadi a tsakanin dukkan Sinawa ciki har da jama’ar jihar Xinjiang, da kuma neman farfadowar tattalin arzikin al’ummar kasar Sin ciki har da kabilu daban daban na jihar Xinjiang. (Zainab Zhang)

 

Exit mobile version