Shafin TASKIRA shafi ne daya saba zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da; zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu. Tsokacin mu na yau zai yi duba ne kan abin da ya shafi samari da ‘yan mata, inda shafin ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiyansa game da wannan batu; “Wasu samarin idan suka tafi wata unguwa kuma suka ga wajen gidansu budurwar su ne sai su biya ta gidansu budurwar, yayin da bangaren ‘yan matan wasu ba sa bukatar hakan dan ba su shirya zuwansu a lokacin ba, hakan na bata musu rai har ta kai ga sun samu sabani da samarinsu. Ko akwai wasu lokuta daya kamata samari su rika zuwa zance wajen ‘yan matansu?, mene ra’ayinku game da wannan batu?. Ga dai bayanan nasu kamar haka:
Sunana Siyama Abdul Jihar Kano:
Eh! akwai lokutan daya kamata samari su ziyarci budurwarsu, domin a komai yana da agogonshi kuma komai sai da tsari ake yin shi, kuma shi ma zance yana daga manya-manyan muhimman abubuwa da za a tsara zuwansu, dan haka mutane su gane cewar zance yana da lokuta. A matsayina na budurwa yadda zan tsara zuwan saurayi wajena ita ce a kalla za mu sami wani ‘yar tazara mai dan nisa, ba wai kullum muna a tare kamar chewing gum ba, don yawan zuwan nan ba wai shakuwa yake kawowa ba sai dai ya sa ku gundiri juna tun ma kafin ayi aure, gara shi namijin ya rinka kewarka, kuma ma yana kawo raini a tsakanin juna don akwai karin maganar da ake cewa “ido wa ka raina- wanda na saba gani”. Shawarar dai da zan bawa samari ita ce, a komai su rinka yin tsari, sannan ba a koyaushe za su rinka ziyartar ‘yan matansu ba dan hakan ya zama zuwan bazata kuma babu kyau zuwan bazata, watakila da sun je gidan za su iya ganin gidan babu tsafta kwata-kwata ko ita kanta budurwar ba da shirin zuwansa ba, karshe idan an yi aure wataran a fara gori musamman daga bangaren mijin.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Jihar Kano Rano LGA:
A nawa raayin hakan ba zai zama lefi ba indai har tsakani da Allah suke son junansu. Lokacin fira daban lokacin ziyara kuwa shi zuwa yake yi babu wani lokaci a yadda na fahimci topic din. Ni dai zan tsara shi ne ranar Alhamis bayan sallar la’asar zuwa sallar magrib idan ma firar ta dauki lokaci sosai kenan ya isa tunda ana waya ko chart. A shawarce hakan sai na ga ba lefi bane duba da an zama daya kuma wannan shi ne zai kara sa nutsuwa a zukatanku na tabbacin kowannenku ya san babu wasu da suke kulawa, sannan zai rage karairayin da ake samu wajen sutura ko gidajenmu ko ababen hawanmu dama abokai ko kawayen da muke kulawa. Allah kasa mu dace.
Sunana Naja’atu Baffa Jihar Kaduna:
Abin da zan ce da samari masu wannan dai’ar zai iya yu wa mutane ne masu son yin bazata a komai kuma a kowanne lokaci, kuma watakila basu da wani isasshen lokaci idan ba wannan lokacin ba. Ni dai a nawa ganin lokacin daya kamata saurayi ya je zance shi ne da fari ya fara tuntubarta su tattauna ya ji lokacin da ta fi sha’awar su yi hira. A nawa tsarin na fi so saurayi ya zo da dare kamar ranar juma’a ko Alhamis, kuma in ya zo ya kamata ya dan yi satika kafin ya dawo tunda yanzu zamani ne na waya ba wai na zirga-zirga ba.
Sunana Umar Babanyaya Sabon-Gida Daga Karamar Hukumar Kafin Hausa A Jihar Jigawa:
Da farko dai batun ware lokaci abu ne mai matukar muhimmanci ga abin da ya shafi soyayya kwarai don haka ya kyautu samari su rinka warewa kansu lokuta na musamman domin hakan zai kara inganta alaka ta soyayya tsakanin masoya. Duk da cewa, ni ban hau gwadaben tsarin soyayya ba, amma na kan tsara lokutan kulawar da zan bawa mata musamman wadda na ga tana sona fatan Allah ya bamu mata nagari. Shawarar da zan bayar ga masoya kuwa ita ce a daina bawa budurwa fifiko kan kannnenku samari, domin mun sani cewa, akwai sabani da wata kila ka iya giftawa tsakaninsu ana da-na-sani Allah ya kyauta.
Sunana Zainab Zeey Ilyas Jihar Kaduna:
Yawan zuwan da samari ke yi wa ‘yan matansu ba komai yake nunawa ba face rashin tabbatacciyyar soyayya, rashin aikin yi, da dai sauran su. Tabbas akwai lokacin da ya kamata mutum ya ziyarci mutum dan’uwanshi ba ma iya tsakanin saurayi da budurwa ba, amma tun da yanzu maganar tsakanin saurayi da budurwa ce to, tabbas su ya kamata ma su fi tsara lokutan. Daya daga cikin tsare-tsaren kuwa su ne; kamar tambayar ta lokacin da ta shirya zuwan, shi namijin ya tambayeta kai tsaye lokutan da ta shirya ganinsa. Shawarar da zan ba wa maza masu yin haka ita ce; a maimakon yawan zuwan nan su tsara ranakun da suka fi dacewa don haduwar su.
Sunana Abubakar Usman Malam Madori:
Wannan matsala da yawa daga cikin ‘yan mata tana ci musu tuwo a kwarya, abun da ya kamata saurayi ya yi shi ne idan har ya fuskanci budurwar sa ba ta san hakan to ya kauracewa yin hakan, domin gudun wata matsala da za ta afku. Ka tabbatar ka sanarwa da masoyiyarka yayin da za ka zo wajenta idan ta amince sai ka je idan kuma ba ta amince ba sai a hakura duk lokacin da ta bukaci hakan sai a hadu. Ni a nawa ra’ayin ba mace ba, ko namiji ban cika zuwa wajen shi ba, ba tare da na sanar da shi ba, domin gudun samun sabani ko rashin samun shi cikin shiri. Ya kamata samari su zama masu tsari a kowanne lokaci ita ma sai ta fi kaunarka. A gaskiya ba za a ware wani lokaci kai-tsaye a ce wannan lokaci ne da ‘yan mata ko samari suka fi son haduwa ba. Sai dai lokacin da suka ware ko suka cimma matsaya ta haduwa ba tare da cutar da kowanne bangare ba. A matsayi na saurayi lokacin da na fi son hira lokuta biyu ne La’asar ko bayan Isha’i zuwa takwas da rabi 8:30. Shawara ita ce; idan har ka fahimci ba ta son zuwanka ba tare da ka sanar da ita ba, to ka yi kokari ka kiyaye domin hakan zai iya shafar soyayyarku ko kuma rashin fahimta a tsakani.
Sunana Amina Abdul’aziz Jihar Bauchi:
Ni dai a nawa ganin lokacin daya kamata saurayi ya je zance shi ne da fari ya fara gane lokacin da ta ke dawowa idan har tana aiki ko zuwa makaranta, sai ya bari in ta dawo ta huta irin da yamma sai ya je, sai kuma weekends, da kuma dare irin bayan mako biyu zuwa wata daya. A ra’ayi na zan duba lokacin da nake ba ni da aiki ko wani nauyi to, awannan lokacin zai iya zuwa. Sannan kuma zamu tattauna don mu fahimci juna, sai musan abin da zai iya fi ma zuwa gidanmu ya ci abincin dare ne da sauransu. Shawarar da zan bawa shi wannan saurayin ya fara tuntubar ita wannan budurwar shin zai iya zuwa a wannan lokacin ko kuwa?, hakan yana nuna abubuwa da yawa kamar ya nuna ka kula da ita, ka girmama ta da dai sauransu
Sunana Jamilu Ibrahim Yandaki Jihar Katsina:
Gaskiya a ra’ayina bai dace saurayi ya kaima budurwasa ziyarar bazata ba, saboda hakan ya kan sa a riskesu kwatsam a yanayin da, da an sanar dasu kafin zuwa ba za su yadda a tarar dasu a hakan ba. ‘Yan mata sukan yi kwalliya tare da tanadi na musamman ga samarinsu yayin da suka sanar dasu zuwansu wanda hakan ya kan kara dankon soyayya da kauna a tsakaninsu, addinin musulunci ma ya hana mutum dawowa gidansa da dare ko kwatsam ba tare da sanarwa ba don gudun taras da iyalinsa ciki halin ba zai ji dadi ba, ballantana kuma budurwa. A ra’ayina akwai lokacin da ya kamata samari su rika zuwa wajen ‘yan matansu shi ne bayan La’asar, sabida a dabi’a a wannan lokacin mutane ba su cika kasancewa a cikin wata hidima ba, sannan lokaci ne mai tsawo zuwa magrib. A matsayina na saurayi gaskiya nafi son na ziyarci budurwata duk ranar Jumu’a bayan La’asar idan hali bai samu ba to sai tsakanin magriba da Isha’i. Shawara musamman ga samari su rika tsara lokuta tare da sanarwar zuwa wajen budurwa kafin lokacin zuwa yayi, tare da bada tazara tsakanin lokuttan zuwa din ya zamana ana samu a kalla kwana hudu ko bakwai, saboda karancin zuwan yana sa ‘yan matan mararin zuwan samarin amma idan ya zamana kowane lokaci ya kan zo wajenta da sanarwa ko ba sanarwa to tabbas soyayyarsu za ta iya samun cikas. Su kuma ‘yanmatan dake da samari masu irin wannan halin su bi hanyar da ta dace wajen fadakar dasu mahimmacin sanarwa kafin zuwa.
Sunana Abdulrahman Jihar Sokoto, Isa LGA:
A gaskiya ni ban da ra’ayin bi ta layin su budurwa ta saboda kowa na da bukatar lokaci a cikin mu kuma gaskiya bai kamata ka zo kwatsam ba ka riske ta a cikin yanayin da ba za ta ji dadin ka ganta a haka ba, kamar yadda kai ma ba za ka so ta gane ka babu shiri ba. Eh, hakikanin gaskiya ya kamata ace akwai agenda da plan na rana da lokacin duwa wajen budurwa. Za mu zauna mu ware lokaci da rana ko sau biyu a rana ne idan hakan yayi daidai a tsakanin mu shikenan. Bai kamata ba ba tsari bane kuma bai cancanta ba babu dacewa a ciki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp