Tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma na daya daga cikin ginshinkin tabbatar da cigaban dukkan al’umma a ko ina a fadin duniyar nan. Haka kuma ‘yansanda ne wadanda aka dora wa nauyin samar da tsaron cikin gida a kowacce kasa a fadin duniya. Rundunar ‘yansandan Nijeriya da Turawan Mulkin Mallaka suka kafa ta gamu da manyan matsaloli tun daga farkon kafata da burin tabbatar da cikakken tsaro ga al’ummar Nijeriya.
Wannan halin da rundunar ta samu kanta ya haifar da sauye-sauye da sake fasali da kokarin kwaskwarima a lokutta daban-daban amma har zuwa yuanzu ba a kai ga samun nasarar da ake bukata ba. Wadannan na daga cikin dalilan da ya sa al’umma suka kasa gamsuwa da yadda ‘yansanda ke gudanar da ayyukansu ba kuma tare da la’akari da dinbin matsalolin da rundunar ke fuskanta ba.
Mambobin Jam’iyyar NNPP 700 Sun Koma Jam’iyyar Labour A Adamawa
Ba tare da kokwanto ba, yadda muke ganin tsananin gurbacewar rundunar ‘yansandan mu yana nuna irin yadda al’ummar mu ta gurbace ne. A Nijeriya an kafa rundunar ‘yansanda ne don kare muradun shugabannin mulkin mallaka na Turawa, sun kafa rundunar ne bayan da suka fahimci cewa, in har suka kafa wata runduna ta musamman zai taimaka musu tatsar albarkatun ma’adanai a sassan kasar nan.
A bayyane yake cin hanci da rashawa ya mamaye al’amurra a Nijeriya amma kuma tsananin cin hanci da rashawar da ake samu a rundunar ‘yansandan yana faruwa ne kai tsaye a kan yadda gwamnati da masu ruwa da tsaki suka dauki tafiyar da harkokin rundunar ‘yansandan. Abin dariya ne in har ‘yan Nijeriya za su yi tunanin cewa, ‘yansanda za su zama kamar malaiku da zarar sun sanya kayan sarki na zama ‘yansanda.
A ra’ayinmu, bai kamata ma a zargi ‘yansanda da karbar na goro a kan hanyoyinmu ba daga ‘yan Nijeriya bayan muna sane da cewa, hatta kayan aikin dake jikinsu sune suke saya da kansu tare da dukkan kayan sarkin da suke amfani dasu a fagen gudanar da aikinsu, wadannan kadai sun isa su ingiza su karbar cin hanci da rashawa don kokarin inganta ayyukansu da rayuwarsu, amma anan ba wai muna halasta karbar cin-hancin da suke yi ba ne.
Duk da kokarin da aka yi na sake fasalin rundunar ‘yansandan Nijeriya a lokutta daban-daban, har yanzu rundunar na nan kamar yadda aka santa a shekarun baya, haka na faruwa ne saboda kokarin da aka yi baya kaiwa ga can kasa inda matsalar take. Shirin sake fasalin rundunar da aka yi a baya yana faruwa ne don biyan bukatun masu mulki a lokacin tare da kuma huce takaici da haushin a bin da suke fuskanta.
Shirin sake fasali na baya-bayan nan an yi shi ne a shekarar 1999, amma ba a kai ga cimma manufar aiwatar da sake fasalin ba, wadanda suka hada da bukatar kare rayuwa da dukiyoyin al’ummar Nijeriya ba tare da nuna banbanci ba, sai dai shirin ya gamu da cikas na rashin cikakken kayan aiki da kuma rashin hadin kai daga bangarori daban-daban.
A shekarar 1989, Admiral Murtala Nyako ya jagoranci kwamitin sake fasalin rundunar ‘yansanda amma a duk tsawon wadannan shekarun ba a kai ga cimma wani abin a zo a gani ba na samar da ingantaciyyar rundunar ‘yansanda da al’ummar Nijeriya za su yi alfahari da ita. Bayan shekara biyu kuma, Farfesa Tekena Tamuno ya mika rahonsa na sake fasalin rundunar ‘yansanda amma har yanzu ba a kai ga yin amfani da su ba.
A shekarar 2006 kuma Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya kafa wani kwamitin karkashin jagorancin tsohon shugaban rundunar ‘yansadan Nijeriya, Muhammad Danmadami. A shekarar 2008 kuma an kafa sabon kwamiti wanda shima tsohon shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya, Muhammadu Dikko Yusuf ya jagoranta, ya kuma samu nasarar mika rahoto tattare da shawarwari 125 na yadda za a inganta aikin ‘yansanda amma har zuwa yanzu ba a kai ga aiwatar da daya daga cikin shawarwarin da suka mika ba.
Haka kuma rahoton kwamitin sake fasalin ‘yansanda da shirin ‘Bision 2010’ ya samar bai samu karbuwa ba a hannun mahukunta. Shima kwamitin da Parry Osayande ya jagoranta a shekarar 2012 bai kai labari ba.
Cin zarafin mutane daga ‘yansanda ba abu ba ne da ya kebu ga Nijeriya, abu ne daya game duk duniya. Amma irin yadda ake sanya ido da kuma yadda ake hukunta wadanda aka samu da laifi shi ne yake banbanta, kamar yadda ake samu a kasashe kamar su Kanada Birtaniya wadanda suka yi fice wajen kare hakkin biladam. Irin rashin hukunta ‘yansanda masu cin zarafin al’umma a Nijeriya yake tayar da hankalin al’umma a dukkan lokutta har yake haifar da zanga-zanga kamar yadda muka gani a lokacin ‘EndSARS, wanda hakan kuma yana shafar mutuncin rundunar. A kan haka muke bayar da shawarar samar da rundunar ‘yansanda mai cikakken kayan aiki na zamani tare da biyansu cikakken hakokinsu ta yadda hankalinsu zai fita daga aikata cin hanci da rashawa.
Tabbas lokaci ya yi da za a sake fasalin rundunar ‘yansandan Nijeriya ta yadda za ta yi daidai da tsarin mulkin dimokradiyya, a tabbatar da sun kawo karshen cin zarafin al’umma, musamnman masu karamin karfi.
Yakamata a yi wa tsarin mulki kwaskwarima ta yadda za a iya dauka da korar shugaban rundunar ‘yansanda kai tsaye ba kamar yadda lamarin yake a halin yanzu ba inda sai abin da shugaban kasa ya ga dama, dole ya zamana majalisar kasa ta sanya hannun a kan zabo wanda zai zama shugaban rundunar ‘yansanda su kuma sanya hannu wajen korarsa in ya gaza gudanar da aikinsa.