• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yaki Da Cin Zarafin Mata Na “EU-UN Spotlight Initiative”: Mun Samu Gagarumin Ci Gaba A Legas – Ibijoke

by Leadership Hausa
2 years ago
Mata

Uwargidan Gwamnan Jihar Legas, Dr. Ibijoke Sanwo-Olu, ta bayyana cewa, sakamakon goyon bayan da suka samu daga shirin Tarayyar Turai (EU) da Majalisar Dinkin Duniya (MDD) na yaki da cin zarafin mata, Jihar Legas ta samu gagarumin ci gaba wajen samar da al’ummar da kowace ‘ya mace za ta iya rayuwa ba tare da tashin hankali ko nuna mata wariya ba.

“Ta hanyar hadin gwiwar da muka yi, mun sami ci gaba sosai wajen samar da al’ummar da kowace mace za ta yi rayuwa ba tare da tashin hankali da wariya ba.” Ta bayyana a wurin rufe shirin na ‘EU-UN Spotlight Initiative’ da aka bullo da shi don kawo karshen cin zarafin mata tare da mika cibiyar da aka samu don wannan aikin ga gwamnatin Jihar Legas a ranar 17 ga Nuwamba 2023.

  • Hukumar Kwastam Ta Kama Kwayoyin Tramadol Na Biliyan N3.55bn A Legas
  • Dalilan Mayar Da Daukaka Kararrakin Zabe 1,209 Zuwa Abuja Da Legas

Bikin da aka gudanar a otal din Airport da ke Ikeja ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da suka hada da kungiyoyin farar hula, daliban Sakandare da dai sauransu.

A cewar Misis Sanwo-Olu, wacce babbar mai ba ta shawara ta musamman kan harkokin cikin gida Misis Motolani Ladipo ta wakilta, Jihar Legas ta ci moriyar hadin gwiwa da kawo sauyi dangane da kawo karshen cin zarafin mata tun bayan kaddamar da shirin na yaki da cin zarafin mata na Tarayyar Turai da Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 2019.

“Jihar Legas tare da goyon bayan sashen mata na Majalisar Dinkin Duniya, da UNDP, da UNESCO, UNFPA da kuma UNICEF a karkashin shirin yaki da cin zarafin mata, ta aiwatar da abubuwa da dama da suka shafi ayyukan gwamnati da suka hada da kafa dokoki da tsara manufofi da ke mayar da hankali kan samun adalci ga wadanda suka tsira daga cin zarafin mata.” Ta bayyana.

LABARAI MASU NASABA

Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI

Batun Umarnin Kotu Na Kama Tsohon Shugaban INEC Ƙage Ne Kawai – Shugaban Jam’iyyar AA 

Uwargidan gwamnan ta yi imani game da nasarar yin aiki tare, inda ta jaddada mahimmancin magance musabbabin cin zarafin mata. Ta kara da cewa, “Bisa himma mai karfi a bangaren rigakafi, kariya, da tabbatar da samun muhimman ayyuka, hadin gwiwa da shirin ‘EU-UN Spotlight Initiative’ yana samar da hanyar da ba za a bar mace babba ko yarinya wajen ci gaba ba a Jihar Legas.”

Kwamishiniyar harkokin mata da yaki da fatara ta Jihar Legas, Ms Cecelia Bolaji Dada, ta bayyana nasarorin da aka samu da kuma muhimman abubuwan da aka cimma a shirin na yaki da cn zarafin mata a Jihar Legas. Ta bayyana yadda suke karfafa ayyuka masu mahimmanci ciki har da kafa asibitocin duba marasa lafiya ta shafin intanet a lokacin annobar COVID19; da karfafa damar samun adalci ga wadanda suka tsira daga cin zarafi, karfafa yekuwar kungiyoyin mata, samar da tallafin gina rayuwa ga wadanda suka tsira daga cin zarafi fiye da 300; da kuma samar da dakin da ake duba wadanda aka ci zarafinsu wanda ya taimaka wajen samar da bayanai a kan shari’ar cin zarafin mata tare da wallafawa a cikin rahoton Ofishin Kididdiga na Kasa.

Babban alkalin jihar Legas, Hon. Kazeem Alogba, ya jaddada muhimmiyar rawar da bangaren shari’a ke takawa wajen magance cin zarafi da nuna wariya ga mata a Jihar Legas.

Da yake magana ta bakin Mai shari’a Abiola Soladoye, ya bayyana mahimmancin kin yin shiru kan abubuwan da suka shafi cin zarafi tare da karfafa wa wadanda suka tsira daga aika-aikar su rika neman adalci ba tare da tsoro ba.

“Bai kamata a yi watsi da miyagun laifukan da ake wa mata ba, kuma idan aka ba da rahoton, wadanda abin ya shafa ka da su yi shakka su fito su fada.” Yana mai bayyana cewa, “‘Yansanda suna da ruwa da tsaki tare da bangaren shari’a wajen taimaka wa dakile lamuran da suka shafi cin zarafin mata.”

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Legas, Mudashiru Obasa, ya jaddada kudirin majalisar na yakar duk wani nau’in cin zarafin mata a jihar.

Wanda Hon. Princess Omolara Oyekan ta wakilta, shugaban majalisar ya jaddada cewa, “Majalisar ba ta daukar duk wani nau’i na cin zarafin mata ta kowace hanya da sanya, sannan kafa hukumar yaki da cin zarafin mata ta Jihar Legas wani muhimmin mataki ne na sadaukarwar da majalisar ta yi don kawar da cin zarafin”.

Ya kara da cewa kokarin da majalisar dokokin Jihar Legas ta yi na samar da dokoki na kare hakkin mata ya sa manyan hukumomi irin su hukumar yaki da cin zarafin mata ta jihar Legas da ma’aikatar mata ta jihar Legas suka yi tsayin daka tare da tsre wa tsara kan kare hakkokin mata.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI
Labarai

Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI

October 9, 2025
Fursunoni Ba Za Su Samu Damar Kada Kuri’a Ba A Zaben 2023 – INEC
Labarai

Batun Umarnin Kotu Na Kama Tsohon Shugaban INEC Ƙage Ne Kawai – Shugaban Jam’iyyar AA 

October 9, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 
Manyan Labarai

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

October 9, 2025
Next Post
Red Cross Ta Yi Sabbin Shugabanni A Adamawa

Red Cross Ta Yi Sabbin Shugabanni A Adamawa

LABARAI MASU NASABA

Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI

Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI

October 9, 2025
Duniya Ta Kara Ganin Bunkasuwar Sin a Lokacin Hutun Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar

Duniya Ta Kara Ganin Bunkasuwar Sin a Lokacin Hutun Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar

October 9, 2025
Fursunoni Ba Za Su Samu Damar Kada Kuri’a Ba A Zaben 2023 – INEC

Batun Umarnin Kotu Na Kama Tsohon Shugaban INEC Ƙage Ne Kawai – Shugaban Jam’iyyar AA 

October 9, 2025
An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin

An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin

October 9, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

October 9, 2025
Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

October 9, 2025
SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

October 9, 2025
An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

October 9, 2025
Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

October 9, 2025
Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.