Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya gana da takwaransa na ƙasar Saliyo, Shugaba Julius Maada Bio, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, da yammacin Juma’a.
Shugaba Bio ya isa fadar Villa da misalin ƙarfe 9:08 na dare, inda aka yi masa tarɓar ban girma, kafin ya wuce ofishin Shugaba Tinubu domin gudanar da ganawar ta sirri.
- Shirin Shugaba Tinubu Na ‘Renewed Hope’ Zai Karfafa Wa Manoma Gwiwa – Oyebanji
- Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Don Karɓo Rancen N1.15trn Don Cike Giɓin Kasafin Kuɗin 2025
An gudanar da tattaunawar ne ƙofa kulle, inda ake ganin manyan batutuwan da suka shafi ƙarfafa dangantakar diplomasiyya, haɗin gwuiwar tattalin arziƙi da tsaro tsakanin ƙasashen biyu, da kuma ci gaban haɗin kai a yankin ECOWAS suka fi ɗaukar hankali.
Taron ya zo watanni hudu bayan da Shugaba Bio ya karɓi ragamar shugabancin ƙungiyar ECOWAS daga hannun Shugaba Tinubu, wanda ya kammala wa’adinsa na shekaru biyu a watan Yuli 2025.
Kawo lokacin haɗa wannan rahoto, ba a fitar da cikakkun bayanan tattaunawar shugabannin biyu ba.














