A yau litinin ake sa ran shugaba Bola Tinubu zai dawo Nijeriya bayan ziyarar aiki da ya kai kasashen Turai, kamar yadda mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga ya bayyana.
Onanuga ya bayyana hakan ne a wani takaitaccen sako da ya fitar a shafinsa na X, yana mai cewa, “Shugaba Bola Tinubu zai dawo gida yau.”
- Hisbah A Katsina Ta Musanta Zargin Cin Zarafin Wata Budurwa A Wani Faifan Bidiyo
- Leicester City Ta Koma Gasar Yan Dagaji Bayan Shan Kashi A Hannun Liverpool
Duk da cewa, fadar shugaban kasar ba ta bayyana takamaiman lokacin da zai shigo kasar ba amma hakan ya kawo karshen cece-kucen da ake yi na tsawon makonni kan rashin shugaban kasa a kasar.
Shugaba Tinubu ya bar Nijeriya ne a ranar 2 ga watan Afrilu zuwa birnin Paris na kasar Faransa, domin wata ‘yar gajeriyar ziyarar aiki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp