Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada muhimmancin ingiza aikin tarbiyantar da yara kanana a fannin karfafa basira da da’a, aikin da ya dace ya kasance bisa manyan tsare-tsare kuma mai matukar muhimmanci.
Shugaba Xi ya kuma yi kira da a hada karfi waje guda, don samar da kyakkyawan yanayi na gina rayuwar yara mai inganci.
Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kuma shugaban hukumar zartarwar rundunar sojojin kasar, ya yi tsokacin ne cikin umarninsa dangane da batun.
Cikin umarnin na shugaba Xi da aka gabatar a yau Litinin, yayin taron karawa juna sani dangane da bunkasa gina basira da da’ar yara kanana, Xi ya jaddada muhimmancin gudanar da tsarin bayar da ilimi na hadin gwiwa tsakanin makarantu, da iyalai da al’umma a fannin raya wannan aiki, ta yadda za a cusawa yara akidar fadada tunanin ci gaba, da aiwatar da muhimman dabi’un gurguzu, da gina da’a mai inganci da kyawawan dabi’u a zukatan yaran kasar. (Saminu Alhassan)














