A kwanakin baya, shugaban kasar Cuba Miguel Díaz-Canel ya yi hira da wakilin rukunin gidajen rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG, inda ya bayyana cewa, kasarsa ta Cuba ta yi nazari kan kwaskwarimar da kasar Sin ta yi, kamar su yadda kasar Sin ta mika iko ga kananan gwamnatocin kasar don sa kaimi ga daidaita harkokin sassan kasar, da daukar jerin matakai wajen yin kwaskwarima a kauyuka don tabbatar da wadatar abinci, da daidaita huldar dake tsakanin manyan tsare-tsare da mika iko ga kananan gwamnatoci, da kuma kasuwanci, da sa kaimi ga raya kimiyya da fasaha da yin kirkire-kirkire, da bunkasa sha’anin al’adu da yawon bude ido a kasar don maida al’adu su zama jigon sha’anin yawon bude ido, da kuma kiyaye maida hankali ga tunawa da tarihi yayin da jam’iyyar Kwaminis ta Sin take jagorancin kasar wajen samun ci gaba.
A ganin shugaba Díaz-Canel, wadannan fannoni shida suna zama matsayi mai muhimmanci da ma’ana, suna bin tunanin raya tsarin gurguzu, kana sun samar da fasahohin Sin ga kasar Cuba wajen sa kaimi ga samun ci gaba a kasar Cuba. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp