Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi hatsarin mota da sanyin safiyar Alhamis a a babban Birnin Kasar Kyiv, amma bai samu wani mummunan rauni ba, in ji sakataren yada labaransa.
Wata mota kuma ta yi karo da motar shugaban kasar daga cikin ayarin motocin da suke rakiyar Shugaban, in ji sakataren yada labaran Zelensky Sergii Nykyforov a cikin wata sanarwa.
“Likitan da ya duba shugaban, yace ba a sami wani mummunan rauni ba ajikinshi”
Direban da ke cikin dayar motar, Likitocin dake ayarin shugaba Zelensky ne suka duba lafiyarsa sannan kuma suka sa shi a motar daukar marasa lafiya, a cewar Nykyforov.
Ya kara da cewa jami’an tsaro na gudanar da bincike kan lamarin.
Zelensky ya ziyarci Izyum da ke arewa maso gabashin Ukraine a ranar Laraba, bayan da sojojin Ukraine suka karbe birnin daga hannun dakarun Rasha a wani bangare na tunkarar hare-haren da suka kai a karshen mako.