Shugaban Makarantar Sakandarin gwamnati da ke Lere a karamar hukumar Tafawa Balewa, Iliyasu Sulaiman da ya umarci matarsa ta sayar da gidansa da motarsa, domin hada kudin fansa ya samu kubutuwa daga hannun masu garkuwa da mutane.
Shi dai Iliyasu Sulaiman mai shekara 50 a duniya ya shafe tsawon kwanaki 8 a hannun masu garkuwa da mutane tun bayan da suka sace shi da karfin tsiya.
Shi dai Iliyasu an yi garkuwa da shi ne bayan da ‘yan bindigan suka tareshi tare da Babban mai binciken kudade na jihar Bauchi Alhaji Abdu Usman Aliyu, lamarin da ya kai ga harbin motar da suke ciki wanda har ya janyo suka illata Oditan sosai da har zuwa yanzu ke kwance a gadon asibiti.
Majiya daga iyalan Shugaban Makarantar sun shaida wa ‘yan jarida cewa a safiyar ranar Asabar din da ta gabata ne Iliyasu Sulaiman Shugaban Makarantar Gobernment Day Secondary School, Lere a karamar Hukunar Balewa ya samu tsira daga ‘yan bindigan da suka sace shi.
Majiya daga iyalan na karawa da cewa, “dan uwanmu dai ya samu tsira inda ya samu dawowa gida.”
Duk da babu wani karin hasken da yayi ga ‘yan jaridan sai dai ya nuna godiyarsu ga dukkanin wadanda suka bada gudunmawa kowace iri ce wajen ganin dan uwan nasu ya samu kubuta daga hannun maharan.
Rundunar ‘yan sanda jihar Bauchi ta bakin Kakakinta Ahmed Wakil sun tabbatar da kubutar Shugaban Makarantar.
Idan dai za ku iya tunawa an jiyo sautin murna na muhawarar da ta kasance a tsakanin ‘yan bindigan da matar Shugaban Makarantar inda har lamarin ya kaisa ga umartar iyalansa da su Saida gidansa da motarsa domin hada kudin fansa, “Ina jin jiki sosai. Ku jinginar da gidana ku kawo musu kudin.” A can gaba kuma ya ce, “Ku saida gidana da motana ku hada kudin don Allah”.
An kuma jiyo matarsa tana korafinku cewa kudin da ake nema a gare su ya yi matukar yawa ba su san inda za su samu kudaden ba, “Malamin makaranta ne wallahi ba mu da ina za mu samu wannan kudin. Dubu 200,000 kawai muka iya hadawa.”
Sai dai har zuwa yanzu babu cikakken bayanin nawa aka biya masu garkuwan kafin suka sako Malamin makarantar. Sai dai a lokacin da suka yi garkuwa da shi, wasu majiyoyin sun ce masu garkuwan sun nemi Miliyan 30 ne a matsayin kudin fansa kafin su sako shi.
Idan za ku iya tunawa mun baku labarin da ke cewa ‘yan bindiga sun harbi Babban mai binciken Kudade na Bauchi tare da yin garkuwa da abokinsa Shugaban Makarantar da kuma dansa.
‘Yan bindigan da ba a san ko su waye ba ne suka harbi Babban Mai binciken kudade na jihar Bauchi (Auditor General), Alhaji Abdu Usman Aliyu a hanyarsa ta dawowa daga kauyensu ta Kardam da ke cikin karamar hukumar Dass.
Sai dai majiyoyin da suka tabbatar da faruwar lamarin ma wakilinmu, sun ce ana zargin ‘yan bindigan sun yi kokarin yi garkuwa da shine, a kokarinsu na yin hakan ne suka bude masa ruwan harsasai.
Lamarin dai ya faru ne a ranar Asabar (23 ga Janairu) a cikin wani daji yayin da ke hanyarsa ta dawowa daga ziyara a kauyensu na Kardam, inda suka bude wuta wa motar wanda suka harbi mutum biyu a ciki tare da garkuwa da mutum guda.
Cikin alhini da kuka, daya daga cikin ‘ya’yan Alhaji Abdu Usman ta yi bayani wa wakilinmu yadda lamarin ya faru daki-daki, inda take cewa: “Su na dawowa a hanyarsu daga Kardam sai wasu dauke da bindigogi wasu da Adduna suka tare su. Nan take direban motar ya yi kokarin juyawa kwatsam sai suka hau harbin motar da bullet suka yi ta harbi.
“Bayan da harbi ya yi yawa sai mutanen cikin motar wadanda sun kai su shida suka nemi direban da ya tsaya. Shi Babanmu, da wani na Miji sai direba da kuma Mata uku ne a cikin motar.
“Su na cikin harbi babu kakkautawa ne suka samu Babanmu a jikin hancisa da kuma jikin wuyarsa.
“Bayan da ‘yan bindigan suka tsaida motar sun kwace wayoyin hannun ‘yan cikin motar. Bayan Babanmu harsashin bindigan ya kuma samu daga cikin matan da suke motar wacce ita harbin ya sameta a cinya.
“Shi direban motar da dayan mutumin ‘yan bindigan sun yin garkuwa da su. Bayan da suka tafi da direban da daya mutumin a yayin da suka bar Babanmu da daya matan cikin jini, Baban namu ya yi ta salati sai wani mai mashin ya zo ya taimaka masa zuwa bakin hanya da yake a cikin daji ne abun ya faru.
“Bayan da ya fito da shi kan titi an hanzarta kaisa asibitin Dass daga can kuma aka dawo da shi asibiti a cikin garin Bauchi, inda yanzu ke jinya.”
Ta ci gaba da cewa direban motar da aka yi garkuwa da shi ya samu ya arce daga hannun masu garkuwan, “Masu garkuwan sun kira wayan iyalan abokin baban mu a yau Lahadi (24 ga Janairun) inda suka ce su na neman fansar naira miliyan 30 kafin su sako shi.”
Ta ce baban nata ya saba zuwa ziyara kauyensu duk ranar Asabar domin duba ‘yan uwa da abokan arziki.
Ta ce, hukumomin tsaro sun sha alwashin bibiyar lamuran tare da tabbatar daukan matakan da suka dace.
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar Bauchi DSP Ahmed Mohemmed Wakil ya tabbatar da faruwar lamarin, “Wasu ‘yan bindiga sun tare kan hanya inda suka kai hari wa Auditor General na jihar Bauchi, Abdu Sule Aliyu.
’Yan bindigan sun yi garkuwa da mutum biyu akwai wani dansa mai shekara 25 da ake Kira Zilkiflu Muhammad da wani mazaunin Dass da ake kira Iliyasu Sulaiman mai shekara 55”.
Wakil ya ce sun dauki Abdul Sule Aliyu zuwa asibitin Dass da kuma dawo da su zuwa asibitin ATBUTH.
Ya bada tabbacin kokarin ‘yan sanda wajen ganin sun kamo wadanda suka yi wannan aika-aikar.
Kawo yanzu dai dukkanin mutum biyu da aka yi garkuwa da su sun tsira da rayukansu yayin da shi kuma Auditor General din ke cigaba da jinyan raunukan da ya samu har zuwa yanzu.