• Leadership Hausa
Saturday, March 25, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shugaban NIS Ya Yi Gargaɗin Biyan Kuɗin Fasfo Da Tsabar Kuɗi A Hannu

…Yayin Da Aka Buɗe Cibiyar Ingantaccen Fasfo Na Yankin Kudu Maso Kudu

by yahuzajere
8 months ago
in Rahotonni
0
Shugaban NIS Ya Yi Gargaɗin Biyan Kuɗin Fasfo Da Tsabar Kuɗi A Hannu
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa, CGI Isah Jere Idris ya yi kira ga ‘Yan Nijeriya masu neman fasfo su tabbatar da cewa sun yi amfani da shafin intanet na hukumar wajen neman fasfo da biyan kuɗi ta nan, ga duk wani fasfo da suke so.

  • Yunkurin Tsige Shugaba Buhari Abin Takaici Ne Matuka —Abdullahi Adamu

Ya yi kiran ne a Fatakwal a yayin ƙaddamar da Babbar Cibiyar Samar da Ingantaccen Fasfo Ta Zamani domin kawar da fasfo na tsohon ya yi a yankin kudu-maso-kudu. Ya bayyana cewa hukumar ta mayar da matakan neman fasfon zuwa shafin intanet ne domin daƙile duk wani nau’i na hada-hadar tsabar kuɗi a hannu wanda ta hakan ne ake ‘yan ƙumbiya-ƙumbiya. Don haka ya buƙaci masu neman fasfon su rungumi amfani da intanet, kana ya yi gargaɗin cewa mahukuntan hukumar za su hukunta duk wanda aka kama yana karɓar tsabar kuɗi a hannu a kan neman fasfo.

fasfo
Jerin manyan bakin da suka halarci kaddamar da cibiyar

Sanarwar da mai Magana da yawun hukumar ta NIS, ACI Amos Okpu ya aike wa LEADERSHIP Hausa ta ƙara da cewa, shugaban hukumar ya yi ƙarin haske kamar haka; “Cibiyar Ingantaccen Fasfo da muke ƙaddamarwa a yau a nan, ɗaya ce daga cikin sauye-sauye da gyaran fuska da muke yi na ƙara inganta sha’anin fasfo ga ‘yan ƙasa. Bisa ƙaddamarwar ta yau, dukkan ofisoshin fasfo na Jihohin Akwa Ibom, Bayelsa, Kuros Riba da Ribas sun sauya daga masu bayar da tsohon fasfo zuwa sabo mafi inganci da aka samar,” in ji shi.

Bisa ƙaddamar da cibiyar dai, dukkan wani mai buƙatar fasfo a cikin waɗannan jihohin, ana sa rai ya cike takardar nema ta shafin intanet a direshin passport.immigration.gov.ng, tare da biyan kuɗi ta nan da kuma neman a ba shi ranar da zai zo a ɗauki bayanansa ta na’ura. Kuma ana buƙatar ya je ofishin fasfon ne kawai a ranar da aka sanya masa.

fasfo
CGI Isah Idris Jere yayin da ake tarbarsa a Fatakwal

Tun da farko, Ministan Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ya bayyana cewa ayyukan fasfo suna da matuƙar muhimmanci da ya kamata a ƙara mayar da hankali a kai sosai.

Labarai Masu Nasaba

NLC Na Shirin Shiga Yajin Aiki Kan Karancin Man Fetur Da Takardun Kudi 

Gudummawar Hajiya Hadiza Bala Usman Wajen Bunkasa Rayuwar Matan Nijeriya

“Fasfo shi ne takarda ta shaidar ƙasa mafi muhimmanci da ya kamata ɗan ƙasa ya mallaka. Ba wai kawai yana bai wa mai shi damar tsallakawa zuwa ƙasashen waje ba ne, yana kuma nuna asalin ɗan ƙasa ne da ‘yancin da yake da shi. Saboda haka, ba wai kawai matakan samun fasfon ya kamata su zama sahihai bisa gaskiya da riƙon amana ba, ya dace waɗanda ke aikin samar da shi su kula sosai da yin abubuwa kamar yadda suka dace,” in ji shi.

Ministan ya yaba wa NIS bisa sauye-sauyen ci gaba da take aiwatarwa a sashen fasfo daga tsohon yayi da ake rubutawa da hannu zuwa na zamani da ake sarrafawa ta na’ura, a yanzu kuma zuwa ingantacce da ake yayi a duniya. Ya nunar da cewa ƙoƙarin da NIS take yi na ganin fasfon Nijeriya ya cika ƙa’idar inganci da Hukumar Sufurin Jiragen Sama ta Duniya (ICAO) ta sharɗanta ba kawai abin yabawa ba ne amma gagarumin ci gaba ne abin alfahari.

Ya ƙara da cewa, sabon ingantaccen fasfon an samar da shi ne da fasahar zamani da ake ya yi a duniya wanda aka ƙawata shi da abubuwa na sirri guda 25 fiye da na wanda ake amfani da shi a yanzu. Sannan takardunsa suna da inganci ta yadda ruwa ba ya lalatawa kuma ‘yan damfara masu buga na jabu ba za su iya kwatanta irin sa ba.

fasfo
Mazaunin manyan baki a wurin taron

Aregbesola ya sake nanata ƙudirin ma’aikatarsa ta ƙin amincewa da cuwa-cuwa da ka iya kawo tarnaƙi ga sauye-sauyen da ake yi inda ya yi gargaɗin cewa duk wani jami’i da aka kama da hannu a ciki zai fuskanci fushin doka. Ya yi kira ga masu neman fasfo su riƙa amfani da shafin intanet wurin gabatar da buƙatunsu tare da tabbatar da bayar da bayanai na gaskiya game da kawunansu domin komai ya tafi daidai-wa-daida.

A halin da ake ciki kuma, Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike wanda mataimakiyarsa, Dakta Ipalibo Banigo ta wakilta a taron, ya yaba wa NIS bisa zaɓar Fatakwal a matsayin Babbar Cibiyar Samar da Fasfo ta yankin kudu-maso-kudu.

Ya ba da tabbacin cewa, jihar ta ƙudiri aniyar bayar da goyon baya ga dukkan hukumomin gwamnati da ke jihar, kana ya yi kiran ɗorewar sauye-sauye da garambawul da ake yi a kan batun fasfo domin ya inganta sosai.

Cikin manyan al’amuran da suka gudana a taron akwai ƙaddamar da cibiyar wacce za ta karaɗe jihohin kudu-maso-kudu da Ministan Cikin Gida Aregbesola ya yi bisa rakiyar mataimakiyar gwamnan Ribas.

Manyan jami’an gwamnati na jihar da na tarayya ciki har da wakilan sojoji da sauran hukumomin tsaro da ke jihar sun halarci taron.

  • https://www.capitalpost.ng/2022/07/nis-rolls-out-enhanced-epassport-for-nigeria-citizens-in-us/

Bisa ƙaddamar da katafariyar cibiyar fasfon dai, yankin kudu-maso-kudu ya bi sahun takwarorinsa na kudu-maso-yamma da wasu cibiyoyi da ke Amurka da Birtaniya wajen sauyawa daga bayar da fasfo na tsohon yayi zuwa sabo.

 

 

 

ShareTweetSendShare
Previous Post

Me Ya Jawo Saurin Ci Gaban Cinikin Waje Na Kasar Sin?

Next Post

Rundunar PLA Tana Ci Gaba Da Atisayen Hadin Gwiwa A Kewayen Taiwan

Related

NLC Na Shirin Shiga Yajin Aiki Kan Karancin Man Fetur Da Takardun Kudi 
Rahotonni

NLC Na Shirin Shiga Yajin Aiki Kan Karancin Man Fetur Da Takardun Kudi 

2 weeks ago
Gudummawar Hajiya Hadiza Bala Usman Wajen Bunkasa Rayuwar Matan Nijeriya
Rahotonni

Gudummawar Hajiya Hadiza Bala Usman Wajen Bunkasa Rayuwar Matan Nijeriya

2 weeks ago
Sin Ta Taya Murnar Bola Tinubu Ya Zama Shugaban Nijeriya
Rahotonni

An Fara Zawarcin Mukaman Siyasa A Gwamnatin Tinubu

2 weeks ago
Zaben Gwamnoni: Jihohin Da Za A Fafata Mai Tsanani
Rahotonni

Zaben Gwamnoni: Jihohin Da Za A Fafata Mai Tsanani

2 weeks ago
‘Yansanda Sun Cafke Mutum 50 Kan Satar Kaya Lokacin Da Gobara Ke Cin Kasuwar Monday Market A Borno
Rahotonni

Waiwaye: Konewar Babbar Kasuwar Maiduguri A Shekarar 1979 Da Sake Gina Ta Da Aka Yi A 1983

3 weeks ago
Sakamakon Zaben Shugaban Kasa Daga Kananan Hukumomin Jihar Bauchi 
Rahotonni

Manyan Abubuwa Takwas Da Suka Girgiza Zaben Shugaban Kasa Na 2023

3 weeks ago
Next Post
Rundunar PLA Tana Ci Gaba Da Atisayen Hadin Gwiwa A Kewayen Taiwan

Rundunar PLA Tana Ci Gaba Da Atisayen Hadin Gwiwa A Kewayen Taiwan

LABARAI MASU NASABA

Najeriya Za Ta Gina Masana`antar Samar Da Kayan Samar Da Wuta Ta Hanyar Hasken Rana

Najeriya Za Ta Gina Masana`antar Samar Da Kayan Samar Da Wuta Ta Hanyar Hasken Rana

March 25, 2023
Mun Kammala Nazari Kan Sakamakon Zaben Gwamnoni – INEC

Mun Kammala Nazari Kan Sakamakon Zaben Gwamnoni – INEC

March 25, 2023
Ramadan: Lokutan Sahur Da Buda-baki Na Azumi Na 4

Ramadan: Lokutan Sahur Da Buda-baki Na Azumi Na 4

March 25, 2023
An Bude Dandalin Tattauna Harkokin Samar Da Ci Gaba Na Kasar Sin

An Bude Dandalin Tattauna Harkokin Samar Da Ci Gaba Na Kasar Sin

March 25, 2023
Burina Masu Basira Su Rika Amfana Da Basirarsu -Haidar Blog

Burina Masu Basira Su Rika Amfana Da Basirarsu -Haidar Blog

March 25, 2023
Rukunin Na’urori Na Biyar Na Tashar Samar Da Wutar Lantarki Ta “Lower Kefu Gorge” Dake Zambiya Sun Fara Aiki

Rukunin Na’urori Na Biyar Na Tashar Samar Da Wutar Lantarki Ta “Lower Kefu Gorge” Dake Zambiya Sun Fara Aiki

March 25, 2023
An Yi Zaman Taron “Kare Hakkin ‘Yan Kananan Kabilu A Sabon Zamani” A Geneva

An Yi Zaman Taron “Kare Hakkin ‘Yan Kananan Kabilu A Sabon Zamani” A Geneva

March 25, 2023
Ra’ayoyin Jam’iyyu Kan Nassarar Abba A Kano

Ra’ayoyin Jam’iyyu Kan Nassarar Abba A Kano

March 25, 2023
Tarihin Zaben Kano: Hannun Karba, Hannun Mayarwa

Tarihin Zaben Kano: Hannun Karba, Hannun Mayarwa

March 25, 2023
Falalar Ramadan Da Wasu Hukunce-hukuncen Azumi

Falalar Ramadan Da Wasu Hukunce-hukuncen Azumi

March 25, 2023
ADVERTISEMENT
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.