• English
  • Business News
Monday, August 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shugaban NPA Abubakar Dantsoho Ya Yi Alkawarin Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya A 2025

by Abubakar Abba
7 months ago
in Tattalin Arziki
0
Shugaban NPA Abubakar Dantsoho Ya Yi Alkawarin Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya A 2025
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A yayin da shugaba Bola Tinubu ya sanar da nada Dakta  Abubakar Dantsoho a matsayin Manajin Daraktan Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA, a ranar 12 ga watan Yulin 2024, masu ruwa da tsaki suka fara yakinin cewar, fannin zai kara tunbatsa maye da yadda yake a baya.

Sai dai, tunain na samun sauki ga fannin ba wai domin Dantsoho ya shafe shekaru yana da kwarewa a fannin bane.

  • Bajintar Aiki: Majalisar Dattawa Ta Jinjina Wa Ministan Yaɗa Labarai
  • Hisbah Ta Yi Kakkausan Gargaɗi Tare Da Kira Ga Iyaye Kan Kula Da Yara Bayan Samun Gawar Wasu 4

Kusan masu ruwa da tsaki a fannin da ke a lungu  da sako na kasar nan, an yi maraba da dadin na Dantsoho, domin sun yi ammmanar cewa, nadinsa, abu ne da ka yi yadda ya dace.

Duba da shekaru 25 da na kwarewa da Dantsoho yake da su a fannin, ya faro aikinsa ne, tun a 1992, a yayin da ya yiwa kasa hidima na shekara daya a wato NYSC, a  Hukumar

Kazalika, kasancewar yana da kwarewa a fannin fasahar kimiyyar harkokin ruwa da kuma ta samar da fasfot din tafiye-tafiyen na kasa da kasa,  hakan ya kara sanyawa, masu ruwa da tsaki a fannin, sun kara aminta da shi.

Labarai Masu Nasaba

NBS Ta Bayyana Dalilin Raguwar Farashin Kaya A Nijeriya

Masu Ruwa Da Tsaki Sun Bukaci Bunkasa Fannin Mai Da Ake Hakowa A Teku

Duba da irin wannan kwarewar da Dantsoho yake da su, babu wata tantama, zai kara samar da dimbin nasarori a fannin a 2025.

Wasu daga cikin jeren nasarorin da ake sa ran zai samar sune, zamanantar da Tashoshin Jiragen Ruwa na kasar, sake sabunta jarjejeniyar zuba hannun jari da kuma gyran kayan da ake aiki da su, a Tashoshin Jiregen Ruwan kasar da sauransu.

A lokacin da ya kama aiki,  matsayin sabon Manajin Daraktan Hukumar, Dantsoho ya yi alkawarin saita Tashohin Jiragen Ruwa na kasar, musamman don ci gaba da bayar da gudunmwarsu, wajen kara habaka tattalin arzikin Nijeriya.

Domin ya tabbatar da wannan alkwarin na sa, tuni dai, Dantsoho, ya kaddamar da nufin bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa na kasar.

Bugu da kari, sa ran da ake yi idan aka saita Tashohin Jiragen Ruwan kasar, hakan zai dora kimasu, a kan gaba a yankin Afrika ta Tsakiya, tare da kuma ture karbe tarhin da Tashar Jiragen Ruwa ta  Abidjan, ke da ita.

Mayar Da Tashar Zuwa Ta Zamani:

Hukumar ta NPA, ta yi namijin kokari wajen wajen mayar da Tashar zuwa ta zamani, tare da kuma daga darajar kayan da ake amfani da su, a Tashar, misali rage cunkso a kofar shiga Tashar da ke a Apapa.

A watan Yulin 2024, Hukumar kaddamar da aikin yin amfani da na’urar zamani a Tashar da ke Onne Port,  wanda hakan ya sanya aka samu kashi 25, na karin kayan da ake saukewa a ajewa a Tasahar.

Sake Gyran Gurin Sauke Kaya Da Ke A Tashar:

A watannin baya, Gwamnatin Tarayya ta nuna bacin ranta kan yadda yanayin wajen sauke kaya ya kaance da ke a Tashar Tin-Can Island  da ke a Jihar Legas.

Hakan ya sanya a Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, a watan Janairun 2024, ya umarci Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje da ta gaggauta gyra wajen, musamman domin a samar hanyoyi, ciki har da gyran ta wajen kaya na Tin-Can Island da ke a Legas.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: DantsohoNPA
ShareTweetSendShare
Previous Post

GDPn Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 5% a Shekarar 2024

Next Post

Motocin Sabbin Makamashi Da Ake Amfani Da Su A Sin Sun Zarce Miliyan 30

Related

NBS Ta Bayyana Dalilin Raguwar Farashin Kaya A Nijeriya
Tattalin Arziki

NBS Ta Bayyana Dalilin Raguwar Farashin Kaya A Nijeriya

3 days ago
Masu Ruwa Da Tsaki Sun Bukaci Bunkasa Fannin Mai Da Ake Hakowa A Teku
Tattalin Arziki

Masu Ruwa Da Tsaki Sun Bukaci Bunkasa Fannin Mai Da Ake Hakowa A Teku

3 days ago
Dalilin Da Ya Sa Gwamnatin Jihar Kuros Ribas Ta Yi Hadaka Da Hukumar NPA
Tattalin Arziki

Dalilin Da Ya Sa Gwamnatin Jihar Kuros Ribas Ta Yi Hadaka Da Hukumar NPA

3 days ago
Ma’aikatan Sufurin Jiregen Sama Sun Bukaci Tinubu Ya Janye Shirin Sayar Da Filayen Jiragen Sama
Tattalin Arziki

Ma’aikatan Sufurin Jiregen Sama Sun Bukaci Tinubu Ya Janye Shirin Sayar Da Filayen Jiragen Sama

1 week ago
NPA Ta Fito Da Sabuwar Doka Kan Kayan Da Ake Ajiyewa A Tashoshinta
Tattalin Arziki

NPA Ta Fito Da Sabuwar Doka Kan Kayan Da Ake Ajiyewa A Tashoshinta

1 week ago
Shirin Iskar Gas Na CNG Abin A Yaba Wa Shugaba Tinubu Ne -Shugaban IPMAN Na Ƙasa
Tattalin Arziki

Shirin Iskar Gas Na CNG Abin A Yaba Wa Shugaba Tinubu Ne -Shugaban IPMAN Na Ƙasa

2 weeks ago
Next Post
Motocin Sabbin Makamashi Da Ake Amfani Da Su A Sin Sun Zarce Miliyan 30

Motocin Sabbin Makamashi Da Ake Amfani Da Su A Sin Sun Zarce Miliyan 30

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Ya Isa Brazil, Zai Nemi Masu Zuba Jarin Biliyoyi A Noma, Makamashi Da Fasaha

Tinubu Ya Isa Brazil, Zai Nemi Masu Zuba Jarin Biliyoyi A Noma, Makamashi Da Fasaha

August 25, 2025

Ɗaruruwan Mambobin APC Sun Sauya Sheka Zuwa ADC A Sokoto

August 24, 2025
Ƴansanda Sun Kama Wani Gawutaccen Ɗan Fashi Da Garkuwa Da Mutane A Nasarawa

Ƴansanda Sun Kama Wani Gawutaccen Ɗan Fashi Da Garkuwa Da Mutane A Nasarawa

August 24, 2025
Za A Bude Cibiyar Watsa Labarai Game Da Bukukuwan Nasarar Yaki Da Harin Japan 

Za A Bude Cibiyar Watsa Labarai Game Da Bukukuwan Nasarar Yaki Da Harin Japan 

August 24, 2025
An Kaddamar Da Makon Fina-finai Da Shirye-shiryen Talabijin Na SCO A Qingdao

An Kaddamar Da Makon Fina-finai Da Shirye-shiryen Talabijin Na SCO A Qingdao

August 24, 2025
CMG Za Ta Gabatar Da Bikin Faretin Soja Na Beijing Cikin Harsuna 85 Ga Duk Fadin Duniya 

CMG Za Ta Gabatar Da Bikin Faretin Soja Na Beijing Cikin Harsuna 85 Ga Duk Fadin Duniya 

August 24, 2025
Akwai Katin Zaɓe Fiye Da Dubu 367 Da Ba A Karɓa Ba A Kano – INEC

Akwai Katin Zaɓe Fiye Da Dubu 367 Da Ba A Karɓa Ba A Kano – INEC

August 24, 2025
An Kaddamar Da Gini Mara Fitar Da Hayakin Carbon Irinsa Na Farko A Duniya

An Kaddamar Da Gini Mara Fitar Da Hayakin Carbon Irinsa Na Farko A Duniya

August 24, 2025
Kasar Sin Ta Gudanar Da Bita Na 3 Na Bikin Cika Shekaru 80 Da Samun Nasara A Yakin Kin Harin Japan

Kasar Sin Ta Gudanar Da Bita Na 3 Na Bikin Cika Shekaru 80 Da Samun Nasara A Yakin Kin Harin Japan

August 24, 2025
Ya Kamata A Kiyaye Sahihin Tarihi Da Rike Gaskiya

Ya Kamata A Kiyaye Sahihin Tarihi Da Rike Gaskiya

August 24, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.