Shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya bayyana gamsuwa game da nasarar da ake samu a aikin ginin sabon majalisar dokoki dake Mount Hampden, karkarar birnin Harare.
Emmerson Mnangagwa ya bayyana haka ne bayan ya yi rangadi a wajen ginin, wanda shi ne rangadi na 5 da ya kai tun bayan fara aikin a watan Nuwamban 2018.
Gwamnatin kasar Sin ce ta samar da kudin gudanar da aikin, wanda rukunin kamfanin gine-gine na Shanghai na kasar ke aiwatarwa.
Sabon ginin, zai maye gurbin tsohuwar majalisar mai kujeru 100 da aka gina tun lokacin mulkin mallaka, wanda a yanzu ya yi wa ayyukan majalisar kadan.
A baya, an sa ran kammala ginin a watan Maris na badi, amma lokacin ya tsawaita zuwa watan Satumba, saboda tsaikon da aka samu sanadiyar barkewar annobar COVID-19. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Allurar Rigakafin Da Sin Ta Samar Na Da Inganci
Ran 30 ga watan Disamba na shekarar bara, bayan allurar...