Jam’iyyar APC da zababben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu sun tabbatar da Sanata Godswill Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa ta 10 da kuma Sanata Jibril Barau a matsayin mataimakinsa.
Hakazalika, sun amince da Hon. Tajudeen Abbas a matsayin shugaban majalisar wakilai da kuma Hon. Benjamin Kalu a matsayin mataimakinsa. Sai dai wannan zabi, kamar yadda wasu dama suka yi hasashe, ya gamu da tutsun sauran masu neman shugabancin majalisun daga APC da wajenta. Yanzu haka masu nema irin su Hon. Wase, Ado Doguwa, Batare da sauransu sun ci gaba da matsa kaimi kan muradunsu.
- Gwamnati Za Ta Kashe Biliyan 22.44 Kan Ciyar Da Fursunoni A 2023
- Sin Ta Bukaci Jami’ar Ofishin Jakadancin Canada A Shanghai Da Ta Bar Kasar
Kafin mu duba irin tsingayen da ‘yan mowar APC da zababben shugaban kasa a kan shugabancin majalisun za su tsallaka kafin su kai bantensu, shin wane ne Sanata Akpabio? Ya yi murabus a gwamnatin Buhari a matsayin ministan kula da harkokin Neja Delta, haka nan tsohon gwamnan Jihar Akwa Ibom daga shekarar 2007 zuwa 2015. Lokacin da yake gwamnan Akwa Ibom ya kawo sauye-sauye na zamani a cikin jihar, inda nan take al’amura suka sauya a wannan jihar, wanda ya kirkiro tsarin karatu kyauta ga kowani yaro dan asalin Jihar Akwa Ibom ba tare da nuna bambancin siyasa, addini ko kabilanci ba. Ya samar da harkokin kiwon lafiya kyauta ga mata masu juna biyu da yara da kuma inganta ababen more rayuwa a cikin jihar.
Sakamakon irin namijin kokari da ya yi a matsayin gwamnan Jihar Akwa Ibom ne al’ummar mazabarsa ta Ikot Ekpene suka zabe shi a matsayin dan majalisar dattawa, inda ya zama shugaban marasa rinjaye a zauren majalisar dattawa a karkashin tsohuwar jam’iyyarsa.
A matsayinsa na shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, Akpabio ya nuna kishin kasa kan yadda ya tafiyar da al’amuran gwamnati da fuskantar ‘yan adawa. Wadanda suka yi tsammanin zai gudanar da makauniyar siyasa ga ‘yan adawa sun ji takaici da salon shugabancinsa. Ya samu damar daidaita matsayinsa na jagoran adawa da bukatar tallafa wa duk wani abu da zai amfanar da ‘yan Nijeriya da jam’iyya mai mulki ta kawo a zauren majalisar dattawa.
Bisa la’akari da dimbin nasarorin da ya samu wanda ba a saba gani ba, a shekarar 2019, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Sanata Akpabio a matsayin ministan ma’aikatan kula da harkokin Neja Delta (NDDC). Aikinsa na farko shi ne, tabbatar da cewa yankin ya kasance cikin kwanciyar hankali, yayin da masu ruwa da tsaki suka sha kai ruwa rana kan hanyoyin da yake bi wajen ciyar da yankin gaba.
A matsayinsa na minista mai kula da ma’aikatan harkokin Neja Delta ya yi duk mai yuwuwa wajen yin abin da ya dace don ganin ya cika buri da muradin al’ummar yankin ta hanyar gudanar da ayyuka masu inganci. Hakan ne ya sa aka fara gudanar da binciken kwakwaf kan ayyukan ma’aikatan wanda aka fara da wanda aka kammala. Tuni dai aka mika rahoton ga gwamnatin tarayya, inda ake sa ran za ta yi amfani da rahoton wajen tsara sabon tsari ga kwamitin da za a kaddamar.
A matsayinsa na ministan ma’aikatar Neja Delta, Akpabio ya samu goyon bayan Shugaba Buhari, ya ba wa yankin wasu sabbin gine-gine 13 da benaye 8 da aka kammala a matsayin hedkwatar ma’aikatan NDDC da aka kammala har ta fara aiki, ya gudanar da ayyuka 52 a yankin Neja Delta, sama da hanyoyi 77 ne ake shirin kaddamar da su a yankin, an kaddamar da rukunun gidajen ‘yansanda a Fatakwal. Sama da gadaje 1000 da ma’aikatar ta gina a jami’ar Uyo ta Jihar Akwa Ibom, yayin da aikin samar da wutar lantarki a Ilaje Ese-Odo da ke Jihar Ondo ke gab da kammalawa kuma ya fara aiki.
Sauran ayyukan da aka kammala sun hada da cibiyar koyon sana’a da ke Agadagba a Jihar Ondo mai gine-gine 38. An samar da jiragen kasa na dakon mai guda 7 na wanda aka kafa a karkashin ruwan Welding Facility a Ibeno a Jihar Akwa Ibom, kamfanin rogo mai sarrafa amfanin gona a Usugbene Irrua a Jihar Edo, cibiyar kiwon lafiya da ke Unguwar Amauzari a karamar hukumar Isiala Mbano ta Jihar Imo, cibiyar lafiya a Odi da ke karamar hukumar Kolokuma/Opokuma a Jihar Bayelsa, aikin gyaran filayeye a karamar hukumar Nsit Attai ta Jihar Akwa Ibom, cibiyar lafiya a Eworkpe da ke Emede ta karamar hukumar Isoko ta kudu a Jihar Delta, aikin gyaran hanyar Umudike-Umueze-Umuoyere kashi na daya a Jihar Ribas, aikin gyaran samar da ruwan sha a Ikot Effiong da ke kauyen Effiong a gundumar Akasoko Clan ta karamar hukumar Akpabuyo a Jihr Kuros Ribas, aikin gina rijiyoyin burtsatse a Ndulu-Amaoba da kuma aikin samar da ruwan sha a karamar hukumar Ikwuano ta Jihar Abiya.
Shi kuwa Sanata Barau Jibrin, gogaggen dan siyasa ne wanda ya kasance mamba a majalisa ta tara daga Jihar Kano, an dai sake zabensa a karo na 3 a jere a majalisar dattawa, kuma ya kasance dan majalisar dattawa mafi matsayi a jamhuriyar tarayyar Nijeriya, ya kasance kan gaba wajen neman wanda zai zama shugaban majalisar dattawa ta 10.
Barau Jibrin, ya yi aure kuma Allah ya albarkace shi da ‘ya’ya da dama, wanda ya kasance dan asalin garin Kabo da ke karamar hukumar Kabo a Jihar Kano.
A shekarar 2017 ne kungiyar ‘yan jaridu ta Nijeriya ta bai wa Sanata Jibrin lambar yabo ta gwarzon sanatan Arewa. Bisa la’akari da irin gudunmawar da ya bayar wajen samar da zaman lafiya, hadin kai, da ci gaban kasa. A watan Oktoba na shekarar 2022, Sanata Barau Jibrin ya samu kyautar lambar girmamawa ta kasa wanda Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya ba shi.
A lokacin zaben ‘yan majalisar tarayya na 1999, sha’awar jama’arsa ne ya zaburar da shi har ya tsaya takarar dan majalisar wakilai ta tarayya a mazabar Tarauni ta Jihar Kano, wanda ya lashe zaben.
A 2015, Sanata Barau ya sake tsayawa takarar har ya lashe zabe a matsayin sanata mai wakiltar Kano ta arewa karkashin tutar jam’iyyar APC. A 2019 da 2023 kuwa, ya sake dawowa zauren majalisar dattawa.
A lokacin da yake matsayin dan majalisar wakilai, ya kasance shugaban kwamitin rabo. Ya kuma kasance mamba a kwamitin kula da wutan lantarki na majalisar wakilai.
A matsayinsa na sanata, an zabe shi a matsayin mataimakin shugaban kwamitin kula da harkokin man fetur na majalisar dattawa, inda daga baya ya zama shugaban kwamitin gaba daya.
A ranar 20 ga watan Yulin 2016, shugaban majalisar dattawa na 8, Dakta Bukola Saraki ya sake fasalin shugabancin kwamitocin majalisar dattawa, wanda aka nada Sanata Barau a matsayin shugaban kwamitin kula da harkokin manyan makarantu.
Bugu da kari, a matsayinsa na dan majalisar dattawa ya taba zama mamba a kwamitocin Neja Delta, masana’antu, sufurin kasa, da kuma rabon kudade, kuma yana taka muhimmiyar rawa a matsayinsa na sakataren kungiyar sanatocin Arewa. A ranar 3 ga Oktobar 2019, ya kawo kudirin doka kan kwalejin kimiyya da fasaha ta Kabo.
Kasancewar Barau a matsayin dan majalisar wakilai da kuma fitaccen sanatan tarayyar Nijeriya, ya kawo sabon sabon salo ga mazabar Tarauni da kuma sanatan Kano ta Arewa, kamar yadda jama’a suka tabbatar sun fuskanci irin wakilci na gaskiya a zauren majalisar tarayyar Nijeriya.
A zaben shugaban kasa na 2023 da aka kammala, Sanata Barau yana Jam’iyyar APC da zababben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu sun tabbatar da Sanata Godswill Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa ta 10 da kuma Sanata Jibril Barau a matsayin mataimakinsa.