A yau Alhamis shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin sun gudanar da taron manema labarai na hadin gwiwa a birnin Beijing.
A yayin taron, shugaba Xi ya jaddada cewa, a bana ake cika shekaru 75 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Rasha. Kuma dangantakar sassan biyu ta zamo muhimmin misali na sabon salon alakar kasa da kasa, da kuma kyakkyawan kawancen manyan kasashe biyu dake makwaftaka da juna. Ya ce, ci gaban bunkasar alakar sassan biyu, na da nasaba da yadda suke dora muhimmanci ga ka’idoji 5.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3, Sun Sace 130 A Zamfara
- Amurka Za Ta Lashe Amanta Game Da Karin Harajin Rashin Adalci Da Ta Bugawa Kasar Sin
Na farko, shugaba Xi ya ce, Sin da Rasha, na dora muhimmanci ga martaba juna a matsayin jigon alakarsu, kuma har kullum suna goyon bayan juna wajen kare manyan muradunsu. Na biyu kuma, sassan biyu suna rungumar hadin gwiwar cimma moriyar juna, a matsayin karfin dake ingiza kawancensu, da aiki wajen yaukaka sabon salon cimma moriya tare. Na uku kuma, Sin da Rasha na kara azamar wanzar da abota a matsayin tushen dangantakarsu, da ingiza kawancensu zuwa mataki na gaba. Na hudu kuma, kasashen biyu na rungume da manufar kyautata tsare-tsare bisa matsayin koli, a matsayin hanyar tabbatar da kawance, da karkata akalar jagorancin duniya zuwa turba ta gari. Na biyar kuma, Sin da Rasha sun himmantu wajen tabbatar da daidaito, da adalci, a matsayin dalilin bunkasa alakokinsu, da mayar da hankali ga warware batutuwa masu jan hankali ta hanyar siyasa.
Sannan a yau shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin sun halarci bikin kaddamar da shekarar al’adun Sin da Rasha, da bikin kide-kide da raye-raye na musamman, wanda aka shirya a birnin Beijing, domin murna cika shekaru 75 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Rasha.
A bana, sassan biyu na Sin da Rasha za su gudanar da ayyukan musayar al’adu masu kayatarwa, don zurfafa hadin gwiwar musayar al’adunsu, da aiki tare, wajen bude sabon babin ingiza musayar al’adu tsakanin Sin da Rasha.
Bugu da kari, a yau Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Rasha Vladimir Putin sun sa hannu, da kuma gabatar da wata hadaddiyar sanarwa, game da karfafa dangantakar abokantakar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a sabon zamani tsakanin jamhuriyar jama’ar kasar Sin da tarayyar Rasha, yayin da ake cika shekaru 75 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasahsen biyu. (Saminu Alhassan, Safiyah Ma)