• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shugabannin Togo Da Cote d’Ivoire Sun Gana Da Ministan Harkokin Wajen Sin

byCGTN Hausa
2 years ago
Togo

Shugaban kasar Togo Faure Essozimna Gnassingbé da shugaban kasar Cote d’Ivoire Alassane Ouattara sun gana da mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi dake ziyara a kasashensu jiya Laraba a birnin Lome da kuma a birnin Abidjan.

A yayin ganawar, shugaba Faure Essozimna Gnassingbé na Togo ya yi karin haske kan dangantakar dake tsakanin Togo da Sin da ma hadin gwiwarsu, ya ce bisa dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka, kasar Togo da sauran kasashen Afirka, sun samu babban ci gaba a fannin samar da kayayyakin more rayuwa. Ya kara da cewa, tattalin arzikin Afirka ya kara bunkasa, an kuma tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a nahiyar Afirka, har ma al’ummun nahiyar na smaun Moriya. Wadannan suna da nasaba da tallafin da kasar Sin ta dade tana samarwa. Togo ta yaba da yadda kasar Sin ke tabbatar da adalci a duniya, da nuna adawa da tsoma baki a harkokin cikin gidan Afirka, da taka rawar da ta kamata wajen samun ci gaban Afirka cikin lumana.

  • Kotu Ta Bai Wa Emefiele Damar Yin Tafiye-tafiye A Nijeriya
  • NIS Shiyyar Arewa Maso Gabas Ta Kaddamar Da “Operation Tsaron Iyaka”

A nasa bangare, minista Wang Yi ya isar da gaisuwar shugaban kasar Sin Xi Jinping ga shugaban kasar Togo, inda ya bayyana cewa, zumuntan dake tsakanin Sin da Togo, ya zama abin misali ga hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa. Sin za ta kara yin hadin gwiwa tare da kasar Togo kan manyan tsare-tsare, da nuna goyon baya ga kasar Togo wajen samun bunkasuwa mai dorewa. Ya ce, karni na 21, karni ne na farfado da kasashe masu tasowa. Kasar Sin za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka tare da kasashen Afirka, da taimakawa kasashen Afirka wajen gaggauta samun ci gaba kansu, da sa kaimi da inganta hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, da kara amfana da sakamakon hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, don samun moriyar Togo da kasashen Afirka.

A wannan rana kuma, Wang Yi ya yi tattaunawa tare da firaministar kasar Togo Mme Victoire Sidémeho Tomégah Dogbé da kuma ministan harkokin wajen kasar Togo Robert Dussey.

Togo
Sannan a yayin ganawar shugaban kasar Cote d’Ivoire Alassane Ouattara da Mr. Wang Yi, Alassane Ouattara ya yaba da hadin gwiwar dake tsakanin kasashensa da Sin, inda ya bayyana cewa kasar Sin ta zama babbar abokiyar cinikayya mafi girma da kuma tushen zuba jari ga kasar ta Cote d’Ivoire.

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Cote d’Ivoire za ta ci gaba da ba da fifiko wajen raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin, a cewar shugaban.

Ya kuma jaddada cewa kasar Sin daya ce tak a duniya, kuma Taiwan wani yanki ne na kasar Sin.

Wang ya ce, bangaren kasar Sin na matukar yabawa irin goyon bayan da Cote d’Ivoire ke baiwa kasar Sin wajen kiyaye dinkuwar kasar da cikakkun yankunanta. Ya kuma bayyana cewa, kasar Sin a shirye take ta sa kaimi ga inganta hadin gwiwar moriyar juna tsakaninta da Cote d’Ivoire.

Ya ci gaba da cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da kasashen Afirka, wajen gano ingantattun hanyoyin da suka dace da yanayin da kasashen ke ciki, da kiyaye ‘yancin kansu, da samar da ci gaba da wadata tare, ta yadda za a cimma nasarar zamanantarwa tare.

Wang ya kuma tattauna da ministan harkokin wajen Cote d’Ivoire a ranar Larabar.

Kasar Cote d’Ivoire ita ce kasa ta karshe a Afirka na ziyarar farko da ministan harkokin wajen kasar Sin ya kai a ketare a bana. Wang ya kuma ziyarci Masar da Tunisiya da kuma Togo yayin ziyarar da ta fara a ranar Asabar. (Zainab Zhang, Yahaya)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Next Post
Ci Gaban Tattalin Arzikin Kasar Sin Mai Dorewa Da Inganci Na Kara Ba Da Gudummawa Ga Ci Gaban Duniya

Ci Gaban Tattalin Arzikin Kasar Sin Mai Dorewa Da Inganci Na Kara Ba Da Gudummawa Ga Ci Gaban Duniya

LABARAI MASU NASABA

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version