Connect with us

RAHOTANNI

Shugabanninmu Suna Da Sauran Aiki A Gaban – Shugaban TAPSA  

Published

on

Alhaji Shu’aibu Abubakar dai shi ne Shugaban masu sayar da shayi na kasa “TAPSA”. Ya tattauna da wakilimmu da ke Jos Lawal Umar Tilde a kan cikar Nijeriya shekaru ashirin da daya da komowa mulkin dimokuradiyya ba tare da sojoji sun yi wani katsalandan ba . Bugu da kari. kuma irin alfanun da aka samu a shekaru ashirin da daya da kasar ta yi karkashin mulkin dimukuradiyya da kuma matsalolin da aka hadu da su a cikin tafiyar ga kuma kuncin rayuwa da al’umma su ke fuskanta a yanzu a sanadiyar annobar cutar Korona, sai kuma wasu al’amura. Ga yadda hirar tasu ta kasance.

 

Nijeriya ta yi bikin murnar cika shekaru ashirin da daya da kafuwar mulkin dimukuradiyya ba tare da sojoji sun jefa kansu cikin mulkar ta ba. kasancewarka daya daga cikin masu burin dandana romon dimukura diyya, ya ya zaka auna rawar da ‘yan siyasarmu ke takawa karkashin mulkin  farar hula?

 

Shekaru shekaru ashirin da daya da kasar nan ko kuma Nijeriya  tayi a karkashin farar hula, zan iya cewa ta wani bangare lalle kwalliya na biya kudin sabulu, amma ta wani bangaren kuma kamata ya yi shugaban kasa da su ‘yan majalisun dokoki na tarayya da na jihohi da Gwamnoni su kara yin kokari wajen yi wa al’ummar kasar nan aiki, domin su sami dandana romon mulkin farar hula, kamar dai yadda suke sa rai kafin zabe,

To, ta bangaren ci gaban kasa kuwa zan iyi cewar an sami nasara wajen  canza tsarin tattalin arzikin kasar a cikin shekaru ashirin da daya da kasar ta yi karkashin mulkin farar hula alal misali  ta bangaren sufuri da kuma sadarwa a nan an sami ci gaba matuka domin an samu abubuwan hawa wanda ya sa harkar jigilar mutane da kayayyaki daga wannan bangare zuwa wancan ya kara inganta. Kuma haka nan ma ta  bangaren sadarwa shi ma an sami cigaba kasancewa samun yalwatar wayoyin hannu mutane sun sami sauki hulda da yan’uwansu.

 

To idan muka koma ta bangaren tsaro yaya ka auna tafiyar?

 

To bangaren tsaro a nan ne nake gani shugabannin da muka zaba suna na da sauran aiki a gabansu sabo da sun gaza wajen kare rayukan ‘yan Nijeriya da dukiyoyinsu domin idan kaduba irin yawan rayuka mutane dake salwanta a yanzu a kullu yaumin ba za a iya lissaftasuba koda yake cigowar wannan gwamnati karkashin jagoranci Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi kokari wajen rage karfin ‘yan Boko Haram, amma abin takaici har yanzu  shi ne ba a iya magance matsalar tsaro a kasar ba, kasancewa bayyanar wadansu kungiyoyin ‘yan ta’adda kamar na masu garkuwa da mutane. Su nemi fansa da na barayin shanu da dai sauransu, musamman ma maganar  abin  da ya fi muni a jihohin Arewaci inda ko wacce wayewar gari sai kaji labarin an kashe mutum.

 

Yadda  kake  daya daga cikin ‘yan kasuwan da ke hulda da kamfanonin da suke samar wa al’ummar kasar nan  da kayayyakin masarufi da na abinci, wacce matsala kake fuskanta a sanadiyar takunkumin da gwamnatoci suka dauka na takaita zirga zirga da killace kasuwanni a sanadiyar annobar Korona?

A nan kafin in ce komai zan fara yaba wa gwamnan wannan jiha ta Filato Barista Simon Bako Lalong, a kan irin kokarin  da gwamnatin sa mai ci yanzu a jihar karkashin jagorancinsa take yi, akan yakar hana yaduwar cutar Koro a jihar da kyautatawa mutane da ya ke yi, a kullun domin Gwamna Lalong, bayan tsayuwar dakan da gwamnati jihar ta yi karkashin jagorancin sa, ke yi wajen yakar  yaduwar Annobar a jihar ya sassauta wa mutane ta hanyar gudanar da harkokin rayuwarsu ta yau da kullun don ya tabbatar da cewar ba wani mutumin dake jihar da ya tagayyara a kan sanadiyar bullar annobar Korona a jihar.

Ko shakka babu idan muka koma da bangaren cikas din da annobar ta haifar wa harkokin kasuwanci a jihar, ba zai iya misiltuwa ba, saboda ya haifar da hauhawar farashin kayayyaki, wanda duk wani kayan da ka sani ana sayar da shi a cikin sauki a kasuwa a ‘yan kwanakin da suka gabata yanzu farashin sa ya yi kusan ninkawa. Saboda kuwa duk irin kayayyakin da kamfanoni suke kawo mana kamar su Fulawa, sikari, madara, shinkafa, Taliya, da dai sauransu yanzu farashin su ya karu da kashi talatin zuwa hamsin.

 

Me za ka ce wa Shugaba Buhari?

Ina taya shugaban kasa Muhammadu Buhari, murnar cikar sa shekaru biyar da fara jan ragamar mulkin kasar, bugu da kari ina kira ga al’ummar kasa da su kara bashi hadin kai da goyon baya, don ya samu kwarin guiwar aiwatar da dimbin ayyukan da suke gabansa kafin nan da karshen wa’adin  mulkin sa  karo na biyu a cika a shekara ta 2023.
Advertisement

labarai