Shugabar kasar Iceland Halla Tomasdóttir, wadda ta halarci taron koli na mata na duniya da aka gudanar a kasar Sin a kwanan baya, ta nuna yabo sosai kan muhimmiyar rawar da Sin ke takawa ta fannin inganta sha’anin mata na duniya, ta kuma bayyana cewa, taron kolin na wannan karo ba kawai yana da babbar ma’ana ga kasar Sin ba, har ma yana da muhimmanci kwarai ga kasashe daban daban na duniya.
Tomasdóttir ta jaddada a yayin da take zantawa da wakiliyar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, wato CMG a takaice, cewa daidaiton jinsi abu ne da ya zama dole a ga ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’umma. Ba wai kawai yana shafar hakkokin mata ba, haka kuma ya kasance zabi mafi dacewa ga kasashe daban daban.














