Hukumar Zaɓen Tanzania ta bayyana Shugabar ƙasa Samia Suluhu Hassan a matsayin wadda ta lashe zaɓen shugaban ƙasa, duk da cewa zaɓen ya gudana cikin tashin hankali da zubar da jini a sassan ƙasar.
A cewar sakamakon da aka sanar da safiyar Asabar, Suluhu ta samu kusan kashi 98 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa, abin da jam’iyyun adawa suka yi watsi da shi, suna kiran sakamakon “bogi” da “wasan kwaikwayo na dimokuraɗiyya.”
- An Kaddamar Da Cibiyar Raya Ilimin Dijital Ta Sin Da Afirka A Tanzania
- Babban Darektan Jaridar The Guardian Ta Tanzaniya: Abubuwan Da Aka Tattauna a Manyan Taruka Biyu Na Sin Na Da Alaka Da Kasashen Duniya
Sai dai jam’iyyar adawa ta Chadema ta ce mutane sama da 700 sun mutu sakamakon tarzomar da ta ɓarke yayin da ake ƙidayar ƙuri’u. Kakakin jam’iyyar, John Kitoka, ya shaida wa kamfanin labarai na AFP cewa mutane fiye da 350 sun mutu a Dar es Salaam, yayin da mutane 200 ke cikin mamata a Mwanza, inda sauran mamatan suka fito daga wasu yankuna na ƙasar.
Kitoka ya bayyana cewa adadin zai iya ƙaruwa saboda doka ta hana fita da aka saka tun ranar Laraba, inda ake zargin jami’an tsaro suna ci gaba da kisa da daddare. Sai dai gwamnatin ta Tanzania ta ƙaryata wannan iƙirari, tana mai cewa adadin da aka bayar “ya yi yawa fiye da gaskiya,” tana kuma musanta zargin keta haƙƙin ɗan adam.
Ministan Harkokin Waje, Mahmoud Thabit Kombo, ya ce wasu tsirarun “’yan ta’adda ne suka haddasa matsalar”, yayin da Sakataren MDD, António Guterres, ya buƙaci a gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa kan zargin amfani da ƙarfin tuwo wajen murƙushe masu zanga-zanga.
Shugaba Samia Suluhu Hassan, wadda ke neman wa’adin ta na farko a hukumance bayan ta gaji marigayi John Pombe Magufuli a 2021, ta tsaya takara ƙarƙashin jam’iyyar CCM mai mulki. Sai dai rashin shigar manyan ‘yan adawa da aka hana tsayawa ko aka daure ya jefa shakku kan ingancin zaɓen da aka gudanar, inda masu zanga-zanga suka yi kira da a kafa gwamnatin riƙon ƙwarya da zai shirya sahihin zaɓe a gaba.














