Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a gun taron manema labaru a yau cewa, shugabar kasar Tanzania Samia Suluhu Hassan za ta zama shugabar kasar Afirka ta farko da za ta ziyarci Sin bayan babban taron wakilan JKS karo na 20.
Bisa labarin da ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayar, bisa gayyatar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi mata, shugabar kasar Tanzania Samia Suluhu Hassan za ta ziyarci kasar Sin daga ranar 2 zuwa 4 ga watan Nuwanba.
Mao Ning ta bayyana cewa, a shekarar 2013, yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ziyarci kasar Tanzania, ya gabatar da tunanin nuna sahihanci ga Afirka, da hadin gwiwa, da goyon baya, da sada zumunta, da kuma daidaita matsaloli tare, a halin yanzu wannan tunani ya kasance tunanin manufofin Sin na raya hadin gwiwa da kasashe masu tasowa.
A shekarun baya bayan nan, Sin da Tanzania sun kara imani da juna kan harkokin siyasa, da samun nasarori kan hadin gwiwarsu, da kuma mu’amala kan harkokin kasa da kasa da yankuna. (Zainab)