Ga duk mai waiwayar yanayi da duniya ke ciki a shekarun baya bayan nan, ya kwana da sanin yadda kalubale daban daban ke addabar sassan kasa da kasa.
Duniya ta jima ba ta fuskanci matsi makamancin wanda ake gani a halin yanzu ba, kana daga barkewar annobar COBID-19, zuwa tabarbarewar tattalin arzikin kasashe da dama, mai nasaba da tasirin yaduwar cutar, zuwa matsalar makamashi, da hatsi da takin zamani, wadanda suka biyo bayan barkewar rikicin kasashen Rasha da Ukraine.
- Kasar Sin Ta Sake Bayyana Matsayinta Kan Rahoton Ofishin OHCHR Dangane Da Jihar Xinjiang
- Malam Ina So A Taimaka Mun Da Maganin Damuwa Da Bakin Ciki?
A yanzu kuma, cutar gyandar biri na kara bazuwa a wasu sassan duniya, wadda ita ma masana ke cewa, tana bukatar matakan gaggawa na shawo kan ta, kafin ta zamewa duniya alakakai.
Masana da dama sun sha bayyana cewa, idan har ana fatan shawo kan wadannan kalubale, da ma makamantansu da duniya ka iya fuskanta a nan gaba, ya zama wajibi sassan kasa da kasa su yi hadin gwiwa da juna, su hada karfi da karfi, bisa manufar “Gudu tare a tsira tare”.
Hakan ne kuma ya sanya a baya bayan nan, muke ganin yadda kasashen nahiyar Afirka ke ta karbar bakuncin manyan jami’ai daga sassan Turai da Amurka, wadanda ke ziyartar nahiyar da nufin karfafa alakar kasashen su da kasashen na Afirka, a wani mataki na fadada damammakin wanzar da hadin gwiwa don bunkasa ci gaba tare.
To sai dai kuma Bahaushe kan ce, “Wanda ya riga ka bicci dole ya riga ka tashi”.
Tuni kasashen Afirka suka jima da kulla kyakkyawar alakar sada zumunta da kasar Sin, da cudanyar al’adu, da amince ta fuskar siyasa, da kafa ginshiki mai karfi na samar da muhimman ababen more rayuwa, karkashin shawarar nan ta “Ziri daya da hanya daya” wadda kasar ta Sin ta gabatarwa duniya.
Kaza lika dandalin raya hadin gwiwa na Sin da kasashen Afirka ko FOCAC a takaice, na daf da cika shekaru 22 da kafuwa, wanda karkashinsa, kasar Sin ke ingiza ci gaban Afirka daga dukkanin fannoni.
A watan Nuwambar bara, bisa kwazon sassan biyu, an yi nasarar gudanar da taron ministoci karo na takwas na dandalin FOCAC a birnin Dakar na kasar Senegal.
Har ma a yayin taron aka amince da kudurori guda hudu, ciki har da sanarwar Dakar.
Kaza lika yayin taron na Dakar, shugaban kasar Sin Di Jinping, ya bayyana kaddamar da shirye-shirye guda tara, da nufin bunkasa hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka.
Makasudin wadannan shirye-shirye kuwa shi ne karfafa kawancen gargajiya, da kara inganta abokantaka, da hadin kai, da gina al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya tsakanin Sin da kasashen Afirka a sabon zamani da ake ciki.
A nata bangare, nahiyar Afirka ta yi tsayuwar daka wajen goyon bayan kasar Sin a dukkanin lokuta a tarihi. Kasashen nahiyar sun amince da manufar “kasar Sin daya tak a duniya”, suna marawa Sin baya, a kokarinta na kare ikon mulkin kai da tsaron yankunanta.
Kaza lika sassan biyu suna tunkarar kalubalen rayuwa a matakin kasa da kasa da na shiyyoyinsu tare.
Tuni dai “Kwalliya ta fara biyan kudin sabulu”, domin kuwa nasarorin da Sin tare da kasashen Afirka ke samu, sun zamo wani ginshiki na kare muradu, da moriyar kasashe masu tasowa.
Sun kuma rungumi dokoki da ka’idojin majalissar dinkin duniya, inda suke yayata muhimmancin cudanyar dukkanin sassa cikin adalci.
A bangaren samar da manyan ababen more rayuwa da Sin ke tallafawa wajen gina su a nahiyar Afirka, an kai ga kammala babbar gadar Foundiougne ta kasar Senegal, da layin dogo na jiragen kasa dake hada birnin Nairobi zuwa Mumbasa, da babbar hanyar mota ta zamani dake birnin Nairobi, da makamanciyarta da ta tashi daga Kribi zuwa Lolabe a kasar Kamaru.
Kana an kaddamar da layin dogo na sufurin jiragen kasa mai aiki da lantarki, wanda aka yiwa lakabi da “10th of Ramadan” a kasar Masar.
Dukkanin wadannan ayyuka bangare ne na bunkasa ikon kasashen Afirka, na inganta ci gaban tattalin arziki, masana’antu, da jin dadin jama’a.
Kasar Sin ta fara cika manyan alkawura da ta dauka, tun bayan wancan taron na Dakar, duk da manyan kalubale da duniya ke ciki.
Karkashin hakan, ta samar da lamuni na sama da dalar Amurka biliyan uku, cikin jimillar dala biliyan 10 da ta alkawarta bayarwa ga cibiyoyin hada hadar kudade dake nahiyar, yayin da ta samar da karin kudaden rance har dala biliyan 2.5, domin gudanar da muhimman ayyukan raya kasa a wasu kasashen na nahiya.
Kaza Sin ta shigar da kudade da yawansu ya haura dala biliyan biyu, cikin jimillar dala biliyan 10, a fannin hada hadar cinikayya tsakaninta da Afirka.
A daya bangaren kuma, kamfanonin kasar Sin sun zuba jarin da ya kai dala biliyan 2.17 a sassan kasashen Afirka.
Hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, ya haifar da gagarumar nasara a fannin dakile kamfar abinci.
A shekarar nan ta 2022 kadai, Sin ta sanya hannu kan yarjejeniyoyin kawar da biyan harajin kwastam tsakaninta da kasashen Afirka 12 kan wasu hajoji da suka kai kaso 98 bisa dari, cikin jimillar hajojin da kasashen ke shigarwa cikin kasar Sin.
Kasashen Djibouti, da Habasha, da Somalia, da Eritrea sun samu tallafin hatsi kai tsaye daga kasar Sin.
Yayin da karin kasashen Afirka ke samun damar shigar da albarkatun gona zuwa Sin.
Karkashin ayyukan kiwon lafiya kuwa, sassan biyu sun gudanar da ayyukan yaki da cutar COBID-19 yadda ya kamata.
Sin ta samar da alluran rigakafin COBID-19 miliyan 189 ga kasashen Afirka 27.
A gefe guda, bisa hadin gwiwar Sin da Afirka, nahiyar Afirka ta kai ga fara sarrafa rigakafin COBID-19, wanda yawansa zai kai kimanin miliyan 400 a duk shekara.
Bugu da kari, ana sa ran kammala ginin helkwatar yaki da cututtuka ta Afirka ko “Africa CDC”, nan gaba cikin shekara mai zuwa.
Wannan kari ne kan cibiyoyi da asibitocin sada zumunta na Sin da Afirka dake kasashe irin su Guinea, da Sudan ta kudu, da jamhuriyar Afirka ta tsakiya, da Chadi, da Malawi.
Masharhanta na ganin ko shakka babu, hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka na da kyakkyawar makoma.
Abun da ake bukata kawai shi ne sassan biyu su rike gaskiya, da amincewar juna.
Su ci gaba da goyon baya, da tallafawa juna kamar yadda suka saba.
Batun tabbatar da ’yancin dukkanin sassan biyu, na ikon mulkin kai da tsaron yankunansu, da wanzar da zaman lafiya da lumana na da matukar muhimmanci ga dorewar nasarorin da suke samu a yanzu.
Don haka kasar Sin ta alkawarta ci gaba da tallafawa kasashen Afirka, ta yadda za su iya warware matsalolinsu da kansu.
Ta kuma sha jaddada manufarta, ta kauracewa tsoma baki cikin harkokin gidan kasashen na Afirka, kamar dai yadda hakan ke kunshe cikin ka’idojin cudanyar kasa da kasa, na akidun majalissar dinkin duniya.
Yayin da Sin da kasashen Afirka ke kan turba ta samun ci gaba tare, ya zama wajibi su zurfafa kawance, da fadada cudanya tsakanin al’ummun su.
Kaza lika yana da kyau, su kara budewa juna kofofin cudanyar al’adu da cinikayya, da cimma moriyar juna a al’amuran duniya baki daya, da ma na shiyyoyi.
A sabon yanayin duniya na yanzu, alamu sun nuna cewa, Sin za ta ci gaba da aiki tare da kasashen Afirka, wajen karfafa ayyukan da aka tsara, karkashin dandalin FOCAC, ta yadda zai zamo silar kara kyautata dangantakar sassan biyu.
Bahaushe kan ce “Da abokin daka a kan sha gari”, ko shakka babu, al’ummun Sin da na kasashen nahiyar Afirka, za su jima suna girbar yabanyar da aka dasa a yanzu, cikin yalwa da aminci.