Sashen sufurin ababen hawa na kasar Sin ya ci gaba da bunkasa yadda ya kamata cikin watanni 5 na farkon shekarar bana, inda alkaluma da dama, ciki har da na yawan fasinjoji, da yawan hajojin dako da aka yi rajista suka karu.
Alkaluman da ma’aikatar sufuri ta kasar ta fitar a Juma’ar nan, sun nuna cewa, tsakanin watan Janairu da Mayun bana, an yi tafiye-tafiye na fasinja da yawansu ya kai kimanin biliyan 25.23, adadin da ya karu da kaso 7.4 bisa dari a shekara.
- Kumbon Chang’e-6 Na Kasar Sin Ya Tattaro Giram 1,935.3 Na Samfura Daga Yankin Duniyar Wata Mai Nisa
- Abubuwan Da Suka Fi Jan Hankali A Taron Koli Na Tsaro A Katsina
A daya bangaren kuma, alkaluman sun shaida cewa, adadin hajojin da aka yi dakonsu ya karu da kaso 4.4 bisa dari, daga na makamancin lokaci na bara, zuwa sama da tan biliyan 16.22, yayin da manyan hajojin da aka yi dakonsu ta jiragen ruwa, suka karu da kaso 7 bisa dari a shekara zuwa tan biliyan 3.86.
Ma’aikatar ta kara da cewa, cikin wa’adin watannin 5, tashoshin ruwa na sufurin hajoji, sun karbi karin kayayyaki daga kaso 4.9 bisa dari a shekara zuwa kusan tan biliyan 7.08, yayin da adadin sundukan dakon kayan dake bi ta tashoshin na ruwa, ya karu da kaso 8.8 bisa dari a shekara, zuwa kwatankwacin kwantainoni masu tsayin kafa 20 har miliyan 132.84. (Saminu Alhassan)