Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD Geng Shuang, ya gabatar da jawabi, yayin tattaunawa kan batun kakaba takunkumi na kashin kai, wanda babban taron MDD ya gudana a jiya Alhamis, inda ya ce, irin wannan takunkumi ya sabawa tsarin mulkin majalisar, da dokar kasa da kasa.
A cewarsa, wasu kasashe kalilan, ciki har da Amurka, suna kakabawa sauran sassa takunkumai na kashin kai yadda suke so, inda suke sanya doka, da shari’arsu gaban na gamayyar kasa da kasa, da na sauran daidaikun kasashe, kuma matakin na lalata ikon kwamitin sulhun majalisar, har ma da keta ka’idar daidaito a tsarin mulki, kana hakan ya zama tamkar tsoma baki cikin hakokin sauran kasashe, wanda ke tozarta manufofi, da ka’idojin tsarin mulkin majalisar.
Geng Shuang ya kara da cewa, kasar Sin ta yi kira ga Amurka, da sauran kasashe da su saurari ra’ayin sassan kasa da kasa, su gaggauta daina kakabawa sauran sassa takunkumi yadda suke so. Ban da wannan kuma, ya yi kira ga al’ummar duniya, da ta lura da mummunan tasiri da wannan batu zai haifar, kana kasashen duniya su yi hadin kai wajen bayyana adawar su da hakan. (Amina Xu)