A safiyar yau Litinin ne, ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya shirya taron watsa labarai mai taken “Tsokacin manyan hukumomin kasar Sin kan zamanintarwa irin na kasar Sin”, inda aka yi bayani kan yanayin da ake ciki wajen dukufa kan ci gaban kasa mai inganci domin zamanantar da kasa mai tsarin gurguza daga dukkan fannoni.
Yayin taron, mataimakin direktan hukumar raya kasa da yin kwaskwarima ta kasar Sin Yang Yinkai ya bayyana cewa, kasar Sin ta samu babban sakamako a bangaren jarin waje a shekarar 2022 da ta gabata, kuma ingancin jarin wajen da aka zuba a kasar, ya karu a kai a kai, kana kasashen da ‘yan kasuwansu suka zuba jari a kasar Sin sun karu, haka kuma yankunan da suka zuba jari a sassan kasar Sin, sun kasance mafi daidaito.
Haka zalika, adadin jarin waje da kasar Sin ta yi amfani da su a zahiri a watan Janairun bana, ya kai kudin Sin yuan biliyan 127.69, adadin da ya karu da kaso 14.5 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara, ana iya cewa, kasar Sin ta bude wani sabon babi a wannan bangare a farkon bana, duk wadannan nasarori sun nuna cewa, masu zuba jari na kasa da kasa, suna cike da imani kan ci gaban kasar Sin matuka. (Mai fassarawa: Jamila)