• English
  • Business News
Friday, October 31, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin Ta Fitar Da Rahoton Take Hakkin Dan Adam A Amurka A Shekarar 2022

by CMG Hausa
3 years ago
Sin

Yau ne, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar da rahoton take hakkin dan Adam a Amurka a shekarar 2022.

Rahoton ya ce, shekarar ta 2022 ta shaida wani gagarumin koma baya ga hakkin dan Adam na Amurka.

  • Girgizar Kasa Ta Kashe Mutum 7, Mutane 60 Sun Bace A Kasar Ecuador 

Ya kara da cewa, a Amurka, kasar da ke yiwa kanta lakabi da “mai kare hakkin da-adam”, cututtuka masu tsanani kamar siyasar kudi, da nuna wariyar launin fata, da matsalar harbin bindiga, da yadda ’yan sanda ke cin zarafin jama’a, da bambanci tsakanin masu arziki da talakawa sun yi kamari.

A cewar rahoton, dokoki na kare hakkin dan Adam, da na shari’a, sun fuskanci mummunan koma-baya, wanda ke kara tauye hakki da ’yancin Amurkawa.

Ranar 27 ga wata, rana ce ta matukar bakin ciki ga wasu iyalan Amurkawa. A wannan rana da safe, ’yan shekaru tara 3 da wasu baligai 3 sun rasa rayukansu cikin harbe-harben da aka yi a makarantar firamare na birnin Nashville da ke jihar Tennessee. Mafarki maras dadi ya sake abkuwa. Ba shakka Amurka ta gamu da matsala.

LABARAI MASU NASABA

Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare

Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Yau Talata kasar Sin ta gabatar da rahoto kan yadda Amurka ta keta hakkin dan Adam a shekarar 2022, wanda ya bayyana wa duniya gaskiyar Amurka.

Rahoton ya yi karin bayani kan yadda aka kara keta hakkin jama’ar Amurka da lalata ’yancinsu a shekarar bara da ta gabata. Amurka ta samu koma baya wajen kiyaye hakkin dan Adam. Ban da haka kuma, rahoton ya ce, Amurka, kasa ce da ta samun harbe-harben bindiga a makarantu. A shekarar 2022 kawai, yawan harbe-harben da aka yi a makarantun Amurka ya kai 302, wanda ya kafa tarihi tun bayan shekarar 1970. Harbe-harben bindiga sun zama babban dalilin da ya haifar da mutuwar kananan yara a Amurka.

Ba a tabbatar da tsaron lafiyar al’ummar Amurka ba, yayin da masu kudi suka yi amfani da kudinsu cikin zabe. Matsalar nuna bambancin launin fata ta kara yin kamari, yayin da gibin da ke tsakanin masu kudi da matalauta yake karuwa. Amurka ta gaza kiyaye hakkin dan Adam a gida. Kuma gwiwar Amurkawa ta sanyaya dangane da salon demokuradiyya da hakkin dan Adam na kasar duka. Amma kuma ’yan siyasar Amurka sun ci gaba da sukar wa wasu kasashe.

Salon hakkin dan Adam na Amurka, mafarki ne mafi rashin dadi na Amurkawa, da ma na al’ummomin kasa da kasa. (Mai fassarawa: Ibrahim, Tasallah Yuan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare
Daga Birnin Sin

Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare

October 31, 2025
Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi

October 31, 2025
An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Kirkire-kirkire Da Bude Kofa Da Raba Damar Samun Ci Gaba A Colombo
Daga Birnin Sin

An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Kirkire-kirkire Da Bude Kofa Da Raba Damar Samun Ci Gaba A Colombo

October 30, 2025
Next Post
Buhari Ya Kaddamar Da Fara Hakar Danyen Mai A Jihar Nasarawa

Buhari Ya Kaddamar Da Fara Hakar Danyen Mai A Jihar Nasarawa

LABARAI MASU NASABA

Yan Nijeriya Na Ɗanɗana Kuɗarsu Kan Jinkirta Cire Tallafin Mai – Sarki Sanusi

Yan Nijeriya Na Ɗanɗana Kuɗarsu Kan Jinkirta Cire Tallafin Mai – Sarki Sanusi

October 31, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Allah Ya Kai Manzon Allah (SAW) Muƙami Na Babban Yabo A Cikin Komai

October 31, 2025
Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare

Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare

October 31, 2025
Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi

October 31, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

October 31, 2025
Matsalar Talauci Da Rashin Tsawon Rai Da ‘Yan Nijeriya Ke Fuskanta

Matsalar Talauci Da Rashin Tsawon Rai Da ‘Yan Nijeriya Ke Fuskanta

October 31, 2025
Matsalar Tsaro: Ko Sabbin Shugabannin Rundunar Soji Za Su Kawo Sauyi?

Matsalar Tsaro: Ko Sabbin Shugabannin Rundunar Soji Za Su Kawo Sauyi?

October 31, 2025
An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Kirkire-kirkire Da Bude Kofa Da Raba Damar Samun Ci Gaba A Colombo

An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Kirkire-kirkire Da Bude Kofa Da Raba Damar Samun Ci Gaba A Colombo

October 30, 2025
An Yi Wa Yara Sama Da Miliyan Biyu Allurar Rigakafin Mashaƙo Da Sankarau A Zamfara

An Yi Wa Yara Sama Da Miliyan Biyu Allurar Rigakafin Mashaƙo Da Sankarau A Zamfara

October 30, 2025
Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma 

Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma 

October 30, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.