Mataimakin ministan ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Sun Weidong, ya gabatar da korafi ga jakadan kasar Koriya ta kudu dake Sin Jung Jae ho, inda ya jaddada adawar Sin, game da kalaman da ba su dace ba, da aka jiyo su daga bakin shugaban Koriya ta kudun game da batun Taiwan.
A ranar Alhamis ne dai Sun Weidong ya yi tsokacin cewa, a kwanan baya, yayin da yake zantawa da manema labarai, shugaban kasar Koriya ta kudu ya bayyana cewa, batun Taiwan bai shafi kasar Sin da Taiwan kadai ba, maimakon hakan batu ne da ya shafi sassan kasa da kasa, kamar huldar dake tsakanin Koriya da kudu da ta arewa.
Game da hakan, Sun ya ce ba za a taba amincewa da kalaman saba doka da shugaban ya furta ba, kuma kasar Sin na matukar adawa da hakan da kakkausar murya.
Sun ya kara da cewa, kasar Sin daya tak ce a duniya, kuma Taiwan yankin kasar Sin ne da ba zai yiwu a balle shi ba. Kana batun Taiwan batun cikin gidan kasar Sin ne, wanda ke shafar babbar moriyar al’ummar kasar Sin, kuma Sin ba za ta yarda a tsoma baki a batun ba.
Ya ce, “Muna bukatar Koriya ta kudu, ta yi biyaya ga ruhin hadadden rahoton kulla huldar diplomasiya dake tsakaninta da kasar Sin, ta nacewa manufar kasar Sin daya tak a duniya, tare kuma da yin abun da ya dace kan batun Taiwan. (Mai fassarawa: Jamila)