An yi kiyasin adadin tafiye-tafiyen fasinjoji tsakanin yankuna zai kai biliyan 4.8 a duk fadin kasar Sin daga ranar 14 ga watan Janairu zuwa ta 2 ga watan Febrairu, wato rabin farko na kwanaki 40 na zirga-zirgar bikin bazara.
Adadin ya nuna karuwar kashi 7.2 cikin dari bisa makamancin lokaci na bara, a cewar tawagar aiki ta musamman da aka kafa don saukake ayyukan da suka shafi zirga-zirgar bikin bazara, wanda aka fi sani da chunyun.
- Hukumar FCTA Ta Rufe Asibitin Da Ke Aiki Ba Bisa Ka’ida Ba A Kuje
- Abinda Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Wasan Athletico Madrid Da Getafe
Zirga-zirgar fasinjoji ya karu tun daga ranar 30 ga watan Janairu, inda adadin tafiye-tafiyen ya zarce miliyan 300 a ranakun 31 ga watan Janairu da ta 1 ga watan Fabrairu, duk sun zarce na bara, a cewar wata cibiyar bincike da ci gaba karkashin ma’aikatar sufuri, tana mai cewa ana sa ran hakan na iya ci gaba da faruwa a lokacin hutun.
Har ila yau, a ranar 2 ga Fabrairu kadai, an yi kiyasin adadin tafiye-tafiye zai kai miliyan 319.32, tare da manyan tituna da ke da kaso mafi girma na tafiye-tafiye miliyan 301.02, a cewar tawagar aiki ta musamman. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)