A yau Litinin, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya ce a ranar Juma’a 25 ga watan nan, aka gudanar da babbar tattaunawar jami’ai, ta murnar cika shekaru 5 da aka gabatar da shawarar inganta ci gaban duniya GDI a hedkwatar MDD dake birnin New York.
Guo, ya ce cikin sakonsa na taya murnar taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce an gabatar da shawarar GDI ne da nufin ingiza hadin gwiwar bunkasa ci gaban duniya, da kara karsashi a turbar bunkasa duniya, da taimakawa wajen gaggauta aiwatar da muradun ci gaba mai dorewa na MDD na nan zuwa shekarar 2030.
Guo, ya kara da cewa irin muhimman matakai, da nasarorin da aka cimma daga shawarar GDI cikin shekaru 5 da suka gabata, sun isa shaida game da aniyar kasar Sin ta ingiza ci gaban bil Adama, da zaman jituwa a duniya, da ma yadda kasar ke kara azamar gabatar da dabarun warware matsaloli, wanda hakan ya mayar da Sin babbar mai samar da gudunmawar ingiza ci gaban bai daya ga dukkanin kasashe.
Sin a shirye take ta yi aiki tare da dukkanin sassa, wajen ci gaba da sauya ajandar SDGs zuwa matakai na hakika, da ingiza manufar gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil Adama. (Saminu Alhassan)














