CRI Hausa" />

Sin Ta Shiga Zamanin Fasahar 5G A Bangaren Kasuwanci

Yau Alhamis 6 ga wata, ma’aikatar masana’antu da sadarwa ta kasar Sin ta sanar da cewa, ta riga ta bayar da takardar izinin amfani da fasahar 5G a bangaren kasuwanci ga wasu kamfanonin sadarwar kasar, wadanda suka hada da China Mobile, da China Telecom, da China Unicom, da China Broadcast Network, lamarin da ya alamta cewa, a hukumance kasar Sin ta shiga zamanin fasahar 5G a bangaren kasuwanci, wato kasar Sin za ta kasance kasuwar fasahar 5G mafi girma a fadin duniya, wadda za ta samar da sabbin damammakin samun ci gaba ga kasar, tare kuma da ingiza sauye-sauyen sana’o’i a kasar, haka kuma za ta samar da sabbin hidimomi ga al’ummun kasar, ta kuma ciyar da tattalin arzikin duniya gaba bisa babban matsayi.
Hakika ba zai yiyu ba, kasa daya ko kamfani daya, ya iya samun sakamako a fannin nazarin fasahar 5G, ko kuma fara amfani da fasahar a bangaren kasuwanci. Yanzu dai an shiga lokaci mafi muhimmanci a fannin tsara ma’aunin fasahar, da nazarin fasahar, da kuma kera na’urori ta hanyar yin amfani da fasahar, kuma abu mai faranta rai shi ne, kamfanonin kasar Sin sun riga sun kai sahun gaba a bangarorin kirkire-kirkire bisa dogaro kansu, da nazarin fasahohi kamar su MIMO, da UDN, da Yanar Gizo Ta Motoci da sauransu, dalilin da ya sa haka shi ne, kasa da kasa sun tsara ma’aunin fasahar 5G ne iri daya a fadin duniya.

Bisa shirin hadin gwiwa kan fasahar 3G wato 3GPP a takaice, wanda hukumar tsara ma’auni ta kasa da kasa ta fitar, an ce, an riga an kammala aikin tsara ma’aunin amfani da fasahar 5G, yanzu kuma an shiga matakin raya masana’antun da ke da nasaba da fasahar, kuma yawan kamfanonin Sin da ke bin ma’aunin fasahar 5G ya kai kimanin kaso 30.
Yayin da kasar Sin ke gwajin amfani da fasahar ta fannin kasuwanci, dimbin kamfanonin kasashen waje kamar su Nokia, Ericsson, Qualcomm, Intel, na sa hannu cikin wannan gwajin da kasar Sin ke yi, lamarin da ya aza harsashi ga yadda kasar Sin ke amfani da fasahar 5G ta fannin kasuwanci.
Za a yi amfani da fasahar 5G domin yin ciniki, kana kamfanonin kasashen waje da dama, ciki hadda kamfanin Nokia, sun shiga aikin raya tsarin fasahar 5G na kasar Sin, wadanda suka shaida cewa, ba za a iya hana samar da fasahar 5G a duniya ba.
Game da batun gwamnatin kasar Amurka ta bukaci kamfanonin kasar Amurka da su hana yin amfani da na’urorin kamfanin Huawei, da samar da kayayyaki ga Huawei, da yin kashedi ga sauran kasashen duniya da su hana yin hadin gwiwa tare da kamfanin Huawei, tashar intanet ta CNN dake kasar Amurka ta bayyana cewa, wannan batu zai kawo hasarorin da yawansu zai kai dala biliyan 11 ga kamfanonin kimiyya da fasaha na kasar Amurka. Shugaban gudanarwa na kamfanin Dialog Semiconductor na kasar Birtaniya Jalal Bagherli ya bayyana cewa, idan aka tsananta yakin cinikin fasahohi, kamfanonin sadarwa ba su da sauran zabi, sai yin hadin gwiwa tare da Sin, wajen nuna kiyayya ga kasar Amurka. Kamfanonin dake fuskantar bunkasuwar sha’anin fasahar 5G sun gano cewa, idan suka yanke hulda da kamfani mafi ci gaban fasahar 5G, za su rasa dama wajen yin takara a nan gaba. (Masu Fassarawa: Jamila Zhou, Kande Gao, Zainab Zhang, ma’aikatan CRI Hausa)[tps_header][/tps_header]

Exit mobile version