Kasar Sin ta yi nasarar harba tauraron dan Adam na Tianhui-5, ta amfani da sabon samfurin rokar Long March-6, daga tashar harba kumbuna ta Taiyuan dake lardin Shanxi na arewacin kasar ta Sin.
Rahotanni sun ce an harba tauraron Tianhui-5 ne da karfe 7 sauran mintuna goma na safiyar Larabar nan, kuma ya shiga falakin sa kamar yadda aka tsara.
- Sin Za Ta Zurfafa Matakan Kare Ikon Mallakar Fasaha Yayin Bunkasa Ci Gaba Ta Hanyar Kirkire-Kirkire
- Hun Manet: Kasar Kambodiya Na Goyon Bayan Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya”
Ana sa ran amfani da tauraron ne domin samar da taswirar kasa, da safiyon albarkatun kasa, da gwaje gwajen kimiyya, da sauran ayyuka masu nasaba da hakan.
Wannan ne karo na 494, da kasar Sin ta yi amfani da rokar Long March domin harba taurarin dan Adam. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp