Wani jami’in kasar Sin ya yi watsi da damuwar da ake nunawa, game da janye jarin waje daga kasar Sin, yana mai jaddada cewa, kasar na da tarin kyawawan sharudda don jawo hankalin masu sha’awar zuba jari daga kasashen waje.
Jami’in ofishin kwamitin kolin JKS mai kula da harkokin kudi da tattalin arziki, ya ce akwai dimbin damammaki na harkokin kasuwancin duniya a babbar kasuwar kasar, da cikakken tsarin masana’antu, da sabbin hanyoyin bunkasuwa.
Jami’in ya ce, GDPn kowane mutum a kasar Sin, ya zarce dalar Amurka dubu 12, kuma rukunin masu matsakaicin kudin shiga, ya zarce miliyan 400, wanda ya samar da babbar kasuwar cikin gida mai dimbin damammaki. Kasar Sin ita ce kasa daya tilo da ke da dukkan nau’o’in masana’antu da MDD ta lissafa, kuma fa’idar da take da su a masana’antu, ba za a hada su da na sauran kasashe ba.
Wannan kalami na zuwa ne, a daidai lokacin da kasar ta gudanar da babban taron kolin raya tattalin arziki na shekara-shekara a makon da ya gabata, don yanke shawarar ba da fifiko kan ayyukan raya tattalin arziki a shekarar 2024. A yayin taron, shugabannin kasar Sin sun yi alkawarin fadada bude kofa mai inganci ga kasashen waje.
A dangane da gaba kuwa, jami’in ya sha alwashin ci gaba da inganta bude kofa, da soke duk wasu takunkumin hana sanya jari ga ‘yan kasashen waje a bangaren masana’antu, da fadada bude kofa a harkokin sadarwa da ma kiwon lafiya.(Ibrahim)