Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a yau Laraba cewa, Sin ta damu da bala’in girgizar kasa da ta auku a Indonesiya.
A jiya ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon ta’aziyya ga takwaransa na kasar Indonesiya Joko Widodo. A cewar Zhao, kasashen Sin da Indonesiya makwabta ne kuma abokan juna, Sin tana son baiwa ayyukan agajin bala’u na Indonesia taimakon da goyon bayan da ya wajaba.
Haka kuma, Zhao ya mai da martani ga kalaman baya-bayan nan da babban sakantaren NATO ya yi game da kasar Sin, inda ya jaddada cewa, bai kamata a yi amfani da ra’ayin siyasa kan hadin kan da ake yi game da tattalin arziki da ciniki ba, hakan ba kawai yana illata muradun bai daya na kasa da kasa ba, ita ma Amurka lamarin zai shafe ta. (Amina Xu)