• English
  • Business News
Sunday, July 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin: Ya Kamata A Girmama Ikon Mulkin Kasa Da Cikakkun Yankunan Kasa Yayin Da Kasashen Duniya Suke Mu’amala Da Juna

by CMG Hausa
3 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Sin: Ya Kamata A Girmama Ikon Mulkin Kasa Da Cikakkun Yankunan Kasa Yayin Da Kasashen Duniya Suke Mu’amala Da Juna
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Kwamitin sulhu na MDD ya shirya wani taro dangane da inganta yin shawarwari da hadin gwiwa a kokarin tabbatar tsaro na bai daya a jiya Litinin bisa shawarar kasar Sin, wadda ke shugabantar kwamitin sulhu a wannan wata, inda Zhang Jun, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD ya shugabanci taron. 

Zhang Jun ya nuna cewa, girmama ikon mulkin kasa da cikakkun yankunan ta, wadda aka tanada cikin kundin tsarin MDD, babban tushe ne na dokokin kasa da kasa na zamanin yanzu, da kuma hulda a tsakanin kasa da kasa. Ya ce idan an kau da kai daga wannan muhimmiyar ka’ida, to, za a hambarar da baki dayan tsarin dokokin kasa da kasa, za a jefa duniyarmu baki daya cikin lokacin duhu, kuma ba za a iya tabbatar da tsaron kowa ba.

  • Babu Nasara Ga ’Yan Awaren Taiwan

Don haka dole ne a fito fili wajen tsayawa kan girmama ikon mulkin kasa, da cikakkun yankunan kasa, da hanyar raya kasa da tsarin zamantakewar al’ummar kasa, wadda jama’ar wata kasa suka zaba da kansu, da kokarin da kasashen duniya suke yi domin kiyaye dinkuwar kasa, da hadin kan al’ummomi.

Wannan ita ce muhimmiyar ka’idar raya hulda a tsakanin kasa da kasa. Haka kuma, babban tushe ne na tabbatar da tsaro na bai daya.

Jami’in ya kara da cewa, har kullum kasar Sin na girmama ikon mulkin kasa, da cikakkun yankunan kasashen duniya.

Labarai Masu Nasaba

Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya

Firaministan Sin Ya Halarci Taron Kasa Da Kasa Game Da Jagorancin AI

Tana kuma mutunta gaskiya da adalci a duniya. Kana tana goyon bayan kokarin da kasashen duniya suke yi wajen kiyaye tsaron bai daya.

Har ila yau, kasar Sin za ta dauki dukkan matakai, na kiyaye ikon mulkin kanta, da cikakkun yankunanta. (Tasallah Yuan)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Nijeriya Da Amurka Sun Kulla Yarjejeniyar Dawo Da Kudaden Da Abacha Ya Wawure

Next Post

“Ɗaukar Abdulkarim Daura Matsayin Mataimakin Gwamna Zai Kawo Wa APC Nasara A Katsina”

Related

Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya
Daga Birnin Sin

Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya

14 hours ago
Firaministan Sin Ya Halarci Taron Kasa Da Kasa Game Da Jagorancin AI
Daga Birnin Sin

Firaministan Sin Ya Halarci Taron Kasa Da Kasa Game Da Jagorancin AI

15 hours ago
An Yi Bikin Karbar Fitilar Gasar Wasannin Kasa Da Kasa Ta Shekarar 2025 A Chengdu
Daga Birnin Sin

An Yi Bikin Karbar Fitilar Gasar Wasannin Kasa Da Kasa Ta Shekarar 2025 A Chengdu

16 hours ago
Sin Ta Gudanar Da Gasar Kirkire-kirkire Ta Daliban Kasa Da Kasa A Yankin Afirka Karo Na Farko
Daga Birnin Sin

Sin Ta Gudanar Da Gasar Kirkire-kirkire Ta Daliban Kasa Da Kasa A Yankin Afirka Karo Na Farko

17 hours ago
Sin Ta Yi Kira Da A Ci Gaba Da Himmatuwa Wajen Warware Batun Ukraine Ta Hanyar Lumana
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Kira Da A Ci Gaba Da Himmatuwa Wajen Warware Batun Ukraine Ta Hanyar Lumana

18 hours ago
Sin Da EU Suna Kokarin Samun Moriyar Juna A Shekaru 50 Masu Zuwa
Daga Birnin Sin

Sin Da EU Suna Kokarin Samun Moriyar Juna A Shekaru 50 Masu Zuwa

2 days ago
Next Post
“Ɗaukar Abdulkarim Daura Matsayin Mataimakin Gwamna Zai Kawo Wa APC Nasara A Katsina”

"Ɗaukar Abdulkarim Daura Matsayin Mataimakin Gwamna Zai Kawo Wa APC Nasara A Katsina"

LABARAI MASU NASABA

Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa

Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa

July 27, 2025
Ƴansanda Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane 6 A Kaduna Da Zamfara

Ƴansanda Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane 6 A Kaduna Da Zamfara

July 27, 2025
aure

Ko Kin San… Matsalolin Mahaifa Da Suke Hana Haihuwa 

July 27, 2025
VON Zai Fara Watsa Shirye-Shirye Da Harshen Sinanci — Ndace

VON Zai Fara Watsa Shirye-Shirye Da Harshen Sinanci — Ndace

July 27, 2025
Yadda Ake Faten Acca

Yadda Ake Faten Acca

July 27, 2025
Hanyoyin Gyaran Gashi

Hanyoyin Gyaran Gashi

July 27, 2025
Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 

Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 

July 26, 2025
Musuluntar Wata Ce Ya Ja Hankalina Shiga Fim – Sailuba Dadin Kowa

Musuluntar Wata Ce Ya Ja Hankalina Shiga Fim – Sailuba Dadin Kowa

July 26, 2025
Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya

Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya

July 26, 2025
Kasar Sin Na Tir Da Harin Isra’ila Kan Makarantu A Gaza Tare Da Kira Da A Dakatar Da Bude Wuta

Isra’ila Na Sanya Alamar Rusau A Dubban Gidajen Fararen Hula A Gaza

July 26, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.