Yayin da ake shirin harba kumbon jigilar kaya na Sin samfurin Tianzhou-6, ta amfani da rokar Changzheng-7, a yau Lahadi an kai wadannan na’urori wurin harba kumbuna na Wenchang da ke lardin Hainan.
Bisa bayanin da ofishin kula da aikin harbar kumbo mai daukar dan Adam zuwa sararin samaniya na kasar Sin ya yi, a halin yanzu, an kammala shirya na’urorin, kuma nan gaba kadan za a gudanar da ayyukan bincike, da gwaji, kafin harbar kumbon bisa shirin da aka tsara. (Zainab)
Talla