Tare da Lubabatu Ya’u
(Aunty Lubaba) Anty Lubabah matar aure ce. Don haka mata zalla (banda maza) za ku iya tura ma ta da tambayoyi ta hanyar imel ko lamba wayar kamar haka: lubabace@gmail.com
Yau ma ga mu a dakin girkinmu Ko kuma in ce madafa, dauke da girki irin na gargajiya.
ALKUBUS
Kayan Hadi
1- Fulawa
2- Mai ko Butter
3- Yis
4- Kanwa ungurnu
5- Gishiri.
Yadda A Ke Hadawa
Uwargida da zarar kin tanadI kayayyakinki sai ki sami mazubi mai kyau ki dauko fulawarki ki tankade a ciki. Sai ki zuba yis a ciki sai ki sami ruwa mai dan dumi ba mai zafi ba.
Sai ki kwaba fulawarki da dan kauri, kamar kwanon fanke, ko ma ya fishi kauri kadan. Kada ki bari ya yi ruwa. Abin nufi kada a cika ruwan. Sai ki sa gishiri ka dan a gurin kwabin yadda zai can fito. Sai ki sa a guri mai dumi ki rufe ki bari har ya kumburo.
In ya kumburo sai ki dauko ki zuba ruwan ungurnu kadan ko in ce ki disa kadan, kana ki sa mai ko butter shi ma ba da yawa ba.
Sai ki sa ludayi ki buga sosai har sai kin ga ya na yin kwayaye sai ki sami gwangwan, ko mazubi ko Leda ki zuzzuba. Amma in mazubi ne ko gwangwani sai kin saka mai a jikin su.
Da ma kin dora ruwan ki a wuta. Dan kadan ba mai yawa ba. Tunda turarawa za ji yi. Sai ki zuba in ruwan ya tafasa sai ki jera a ciki. Bayan kamar minti uku ko hudu zuwa biyar sai ki sami toothpick ki dan zira a ciki.
In kinga kin zaro babu kullin a jiki to ya dahu, in kuwa da kullin a jiki to bai da huba. Kada a bari ya yi ta dahuwa saboda in ya dade zai koma ya kwana daga kumburiñ da ya yi. Iya ci da ko wacce miya, badda miyar yauki.
SINASIR
Kayan Hadi
1- Shikafar tuwo
2- yeast
3- Gishiri
4- Sugar
5- Mai
Yadda A Ke Hadawa
Bayan kin wanke shinkafarki tsaf, sai ki sami dafaffiyar shinkafa, ko bayan tuwo kadan ki saka a cin shinkafar ki biyar a markado su tare. Sai ki kawo yis ki zuba ki ajiye a guri me dumi ya dan tashi kana ki sami abin suya me fadi na sugar sinasir ki dora a wuta.
Sai ki zuba gishiri da sikari de de dandano ki buga. Da ma kin shafa mai kadan a jikin tanadar sai ki zuba kullum ki sami murfi ki rufe.
Ki barshi mintina kadan sai ki bude, za ki ga saman ya yi ‘yan kofofi sai ki dauke. Ba a juyawa. Haka za ki yi ta yi har ki gama.
KISRA
Kayan Hadi
1- Dhinkafar tuwo
2- Yeast
3- Nono
4- Sugar
5- Gishiri
b- Mai
Yadda A Ke Hadawa
Kamar yadda a ke kabin sinasir haka za ki yi uwargida sai dai shi in ki sa his din za ki dan zuba mono, don ita a na son ta dan yi tsami kadan a baki.
Uwargida, in ki na son kullin ki ya yi saurin tashi ki ringa saka his din a cikin shinkafarki kafin a markado. Za ki iya yin hakan ma a markadan sinasir din ko na waina.
Idan kin zo wajen yin suya in kin goga mai a tandar, to shi kullin ma gogawa a ke yi ba a cika shi kamar sugar sinasir. To, gogawa ake yi, saboda a na son ta yi fale-fale sosai. Shi ma ba a juyawa.