Khalid Idris Doya" />

Sojoji Sun Cafke Mutum 27 Bisa Zargin ‘Yan Kungiyar Asiri Ne A Jos

‘Yan Kungiyar Asiri

Rundunar soji a karkashin tawagar Operation Safe Haben sun samu nasarar cafke mutum ashiri da bakwai bisa zarginsu da kasancewa a kungiyoyin asiri a jihar Filato.

Kwamandan rundunar, Manjo Janar Chukwuemeka Okonkwo, wanda ya baje kolin wadanda suke zargin a shalkwatarsu da ke Jos a jiya Asabar, ya shaida cewar sun kuma samu nasarar cafke wasu gungun masu safaran miyagun kwayoyi a yayin samamen da suka kaddama inda suka mika su ga hukumar dakile sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA domin daukan matakan da suka dace.

Ya ce dukkanin wadanda suke zargin da suka hada da mata shida, sun cafke su ne a yayin da rundunar ta kaddamar da samame a maboyarsu da ke sassa daban-daban na Jos ciki kuwa har da otel-otel daga ranar 17 zuwa 20 ga Nuwamba.

Kwamandan ya bada tabbacin hukumarsu na cigaba da kokarin tsarkake jihar Filato daga aikace-aikacen migayi da ‘yan ta’adda.

“Za mu cigaba da cafko masu garkuwa da mutane, ‘yan kungiyar asiri, da sauran miyagu domin babu wani wurin da za su boya da ba za a mu bankado ba.

“Mu na kira ga al’umma da suke samar mana da bayanan miyagu a kowani lokacin domin sauwaka mana wajen gudanar da ayyukan da suke gabanmu,” a cewar kwamandan.

Exit mobile version