Dakarun sojin Nijeriya sun ceto wasu mata uku da aka yi garkuwa da su tare da kwato makamai a yayin wasu hare-hare da suka kai wa ‘yan ta’adda a jihohin Katsina da Zamfara.Â
Sojojin sun samu nasarar dakile wasu ayyukan ta’addanci bisa bayanan sirri da suka samu, ciki har da tare hanya da maharan suka yi kokarin yi.
- Tsarin BRICS Na Samun Karin Karbuwar Kasashe Daban-Daban
- An Gudanar Da Taron Tattaunawar Kafofin Watsa Labarai Na Kazan Na Kasashen BRICS
A Jihar Zamfara, sojojin sun dakile shirin kulle hanya da maharan suka yi a ranar 21 ga watan Oktoba, 2024.
Dakarun sun yi artabu da ‘yan ta’addan, wanda hakan ya sa suka tsere suka bar wasu makamai da alburusai.
Haka zalika, sun yi nasarar kai hari kan wata tawagar ‘yan bindiga a Jihar Sakkwato, inda suka kwato karin alburusai da kayayyakin aiki.
A Jihar Katsina, sojojin sun dakile wani hari da aka kai kauyen Damari, inda suka ceto mata uku da aka yi garkuwa da su.
Dakarun sun sake hada matan da iyalansu cikin koshin lafiya.