Sojojin Nijeriya sun ceto wata ‘yar makarantar Chibok mai suna, Ruth Bitrus, da aka yi garkuwa da ita tare da wasu da dama daga makarantar Sakandaren ’yan mata ta gwamnati ta Chibok da ke Jihar Borno a ranar 14 ga Afrilu, 2014.
Wani rahoton sirri da Zagazola Makama, masani a fannin yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi, ya samu daga majiyar sojin, wanda ya riski wakilinmu, ya nuna cewa Sojojin Birged 21 masu sulke ne suka ceto Ruth da danta a Bama, jihar Borno ranar Laraba, 29 ga watan Yuni, 2022, bayan ta tsere daga hannun mayakan Boko Haram a yankin karamar hukumar Bama ta jihar.
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Boko Haram 3 Da Kwato Makamai A Wani Farmaki Da Suka Kai Musu
- ‘Yan Boko Haram 204 Sun Mika Wuya Ga Sojoji A Jihar Borno
A yayin da take bayar da labarin irin halin da ta shiga, Ruth ta ce ta tsere daga dajin Sambisa shekaru takwas bayan da ‘yan ta’addar Boko Haram suka sace ta daga makarantarta da ke garin Chibok.
Ta ce bam ne ya kashe mijin ta ‘dan ta’adda a lokacin da yake kokarin tayar da shi a kan dakarun Operation Hadin Kai da ke yankin Arewa maso Gabas.
Ruth ta kara da cewa har yanzu sauran ‘yan matan makarantar na tare da wadanda suka yi garkuwa da su a dajin Sambisa.
“Na dauki kwanaki uku ina tserewa daga yankin ‘yan tada kayar bayan. Na dauki abinci da zamu ci ni da yarona. Wasu daga cikin ‘yan Boko Haram sun ganni a lokacin da nake fitowa amma sai na gudu daji don gudun kada a kama ni,” inji ta.
Idan dai za a iya tunawa, makonni biyu da suka gabata ne Sojojin suka kubutar da wasu ‘yan matan makarantar Chibok guda biyu, Mary Dauda da Hauwa Joseph, bayan da suka tsere daga sansanin Gazuwa, hedikwatar kungiyar Jama’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihād da aka fi sani da kungiyar Boko Haram. Gabchari da Mantari da Mallum Masari da ke da nisan kilomita tara zuwa karamar hukumar Bama ta jihar Borno.
Kubucewar nasu ya biyo bayan gagarumin farmakin da dakarun Operation Hadin Kai suka ci gaba da kaiwa, wanda ya janyo yunwa da kaura a yankunan ‘yan ta’addan.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, Boko Haram ta yi garkuwa da dalibai mata 276, masu shekaru tsakanin 16 zuwa 18 a makarantar Sakandaren ’yan mata ta gwamnati da ke garin Chibok a Jihar Borno a watan Afrilun 2014.
Sama da 100 daga cikin ‘yan matan makarantar ne har yanzu ba a san inda suke ba tsawon shekaru takwas bayan da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su.