Dakarun bataliya ta 159 ta sojoji da ke Geidam a Jihar Yobe sun tare wata mota dauke da fakiti 98 na tabar wiwi na miliyoyin Naira.
Birigediya Janar Umar Muaza, shugaban ma’aikata na sashin Hadin Kai da ke Damaturu ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Litinin a yayin mika kayayyakin baje kolin ga jami’an hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) a jihar.
- Da Dumi-Dumi: Dan Majalisar Katsina Ya Rasu A Saudiyya
- Karbuwar NNPP A Karamin Lokaci Alama Ce Ta Nasara A 2023 – Sanata Hanga
Ya ce dan aiken da ke jigilar haramtattun kwayoyin ya yi watsi da motarsa, ya yi ta kai-komo lokacin da ya hangi dakarun da ke sintiri.
Da yake karbar fakitin guda 98 da aka kama a madadin hukumar NDLEA reshen jihar Yobe, Ogar Peter, ya ce farashin kowane fakiti ya haura N50,000.
“Mun yi matukar farin ciki da cewa, an gano wannan adadin daga wurare daban-daban. Idan da ta je inda ta ke ta karshe, da an yi amfani da ita wajen rura wutar kalubalen tsaro,” in ji shi.
Peter ya kara da cewa kamun da sojojin suka yi na miyagun kwayoyi ya nuna irin hadin kai tsakanin hukumomin tsaro da ke aiki a jihar.
“Rundunar sojin Nijeriya na bayar da goyon baya sosai a fafutuka da kuma yaki da matsalar safarar miyagun kwayoyi.
“Za mu ci gaba da kwankwasa kofarku don neman hadin gwiwa da taimako,” in ji shi.