Sojoji tare da taimakon ‘yan sa-kai, sun kashe sama da ‘yan bindiga 100 a wani harin kwanton-É“auna da suka kai Æ™auyen Warari, a Jihar Neja.
Fafatawar ta faru ne a ranar Talata, bayan da sojojin suka samu sahihan bayanai daga mazauna yankin game da hanyoyin da ‘yan bindigar ke bi don satar shanu a kan babura.
Bayan samun wannan bayani, sojojin suka shirya harin kwanton-É“auna, inda suka yi artabu da ‘yan bindigar tare da kashe da dama daga cikinsu.
Wasu shaidu sun shaida wa manema labarai cewa sojojin sun zo da manyan motoci masu sulke da makamai na zamani, abin da ya taimaka musu wajen samun galaba a kan ‘yan bindigar.
Shugabannin al’ummar Warari sun ce sun ga gawarwakin ‘yan bindiga sun a kan tituna, gonaki da kuma dazuka da ke kusa da yankin, wanda ke nuna irin asarar da suka yi.
Jihar Neja na É—aya daga cikin jihohin da ke fama da matsalar ‘yan bindiga da ke kashe jama’a da yin garkuwa da su don neman kuÉ—in fansa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp