Rundunar Sojojin Nijeriya sun yi nasarar kashe wasu manyan shugabannin ‘yan bindiga biyu da ake nema ruwa a jallo, Baldo da Baban Yara, tare da sauran yaransu.
Shugabannin sun kasance manyan tawagogi a yankin da ke musayar wadanda aka yi garkuwa da su a sansanonin jihohin Zamfara ko Katsina.
- Hanyoyi Goma Da Za Su Taimaka Wajen Gyaran Jiki
- Yawan Marasa Aikin Yi A Nijeriya Ya Karu Da Kaso 5 A Karshen 2023 – NBS
Wata majiyar leken asiri ta tsaro ta tabbatar wa PRNigeria cewa, an kashe ‘yan ta’addan ne a ranar Asabar a wani kazamin farmakin da sojoji suka kai a yankin Zamfara ko Katsina.
Talla
A cewar wata majiya mai tushe ta shaidawa PRNigeria cewa, an gudanar da harin cikin nasara domin babu wani dan ta’adda da ya tsira.
Talla