Shalƙwatar Tsaro ta Nijeriya (DHQ) ta bayyana cewa Sojojin ƙasar da ke aiyukan cikin gida sun kama ƴan ta’adda, da ƴan fashi, da sauran miyagu 450, tare da ceto mutane 180 da aka yi garkuwa da su a cikin watan Satumba.
Daraktan yaɗa labarai na rundunar tsaro, Manjo Janar Markus Kangye, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, inda ya ce Sojojin sun kuma karɓi masu laifi 39 da suka mika wuya, tare da kwato ɗanyen mai da darajarsa ta kai ₦112,175,220.
- Sojoji Sun Kashe Mayaƙan ISWAP, Sun Kama Wasu Da Miyagun Ƙwayoyi
- Makaman Rasha Masu Gudun Walkiya Da Ke Yi Wa Ƙasashen Turai Barazana
Kangye ya ce Sojojin sun ƙwato makamai 63, da harsasai 4,475, da wasu kayan fashewa 294, motocin ƴan ta’adda, da babura, da na’urorin sadarwa da ake amfani da su wajen aikata laifuka. A yankin Kudu maso Kudu, ya ce dakarun sun kuma kwato lita 49,321 na ɗanyen mai, lita 6,970 na dizel, lita 1,900 na kerosene, da lita 1,475 na fetur, tare da lalata wuraren tace mai 41 da ba bisa ƙa’ida ba.
A cewarsa, an kuma gano manyan bindigogi, da RPG, da makaman da aka ƙera a gida, da kayan haɗa abubuwan fashewa a wuraren da aka kai farmaki.
Janar Kangye ya tabbatar da cewa aikin yaƙi da ta’addanci na ci gaba, kuma kwamandojin da ke filin daga za su ci gaba da nazarin halin da ake ciki don tabbatar da zaman lafiya da hana sake tashin tarzoma. Ya ƙara da cewa rundunar tsaro tana aiki ne cikin bin doka da ƙa’idojin ƙasa da na duniya, tare da mayar da hankali kan kare rayukan jama’a da na Sojoji a dukkan fannonin aikin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp