Dakarun runduna ta 1, reshen Sector 2 na atisayen Fansar Yamma, sun samu nasarar kashe wani babban shugaban ‘yan ta’adda, Alhaji Ma’oli, tare da wasu mayaƙansa a jiya 26 ga Disamba, 2024, a Jihar Zamfara.
Wata sanarwa daga Ko’odinetan Sadarwa na haɗin gwuiwa, Laftanar Kanal Abubakar Abdullahi, ta bayyana cewa dakarun sun kai farmakin ne a ƙauyen Mai Sheka, kusa da garin Kunchin Kalgo, wanda ya sha fama da baƙin mulkin zaluncin Ma’oli.
- Sokoto Ta Amince Da Kashe Naira Biliyan 15 Ga Gyaran Makarantu, Motocin Alkalai Da Sauransu
- Gwamnatin Tarayya Ta Ɗage Haramcin Haƙar Ma’adanai A Zamfara
Ma’oli ya shahara wajen ƙaƙaba harajin zalunci ga mazauna unguwannin Unguwan Rogo, Mai Sheka, da Magazawa, a yankin Bilbis na ƙaramar hukumar Tsafe.
Sanarwar ta ƙara da cewa kashe Ma’oli ya kawo sauki da farin ciki ga mazauna yankin. Dakarun sun gudanar da wannan farmakin ne bayan samun bayanan sirri kan ‘yan ta’adda masu aiki da babura a yankin Bilbis, inda suka yi nasarar daƙile shirin kai hari ga al’ummar yankin.
Dakarun sun kuma tabbatar da aniyar su ta kare yankin daga duk wani aikin ta’addanci a nan gaba.