Dakarun Sojin Nijeriya sun kashe ‘yan bindiga 45 a wata fafatawa da suka yu a Æ™auyen Iburu, da ke Æ™aramar hukumar Shiroro a Jihar Neja.
Rahotanni sun ce sojoji tare da wasu Æ™wararrun jami’an tsaro sun yi wa ‘yan bindigar kwanton É“auna a yammacin ranar Juma’a, inda aka yi artabu mai zafi.
- Sin Da Benin Da Thailand Za Su Aiwatar Da Matakan Saukaka Tantance Kaya Na Kwastam
- Xi Ya Yi Kira Da A Yi Azamar Kare Rayukan Al’umma Yayin Da Ake Fuskantar Ibtila’in Ambaliya A Wasu Sassan Kasar Sin
A yayin arangamar, sojoji biyu sun rasu.
Wannan samamen na cikin jerin fafatawa da ake yi da ‘yan bindiga a Arewa Maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, inda suka hana manoma sakat kuma suka jefa al’umma cikin Æ™unci.
A watan Yuli, sojoji sun kuma kashe ‘yan bindiga 95 a wani hari na sama da Æ™asa a Jihar Neja.
Rundunar sojin ba ta fitar da sanarwa ba game da wannan hari na baya-bayan nan, amma hukumar DSS ta tabbatar da faruwar lamarin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp